Bola Tinubu Ya Samu Babban Mukami, Kungiyar AU Ta Ba Shi Nauyi a Nahiyar Afrika

Bola Tinubu Ya Samu Babban Mukami, Kungiyar AU Ta Ba Shi Nauyi a Nahiyar Afrika

  • Bola Ahmed Tinubu ya samu matsayi daga kungiyar AU, an nada shi gwarzon harkokin lafiya a Afrika
  • Hukumar CDC ta aiko takarda zuwa Ma’aikatar kasashen wajen Najeriya inda ta sanar da nadin mukamin
  • Kungiyar AU ta yi la’akari da kokarin Mai girma Bola Tinubu a bangaren lafiya bayan zama shugaan kasa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya zama gwarzon kiwon lafiya a nahiyar Afrika a sakamakon mukamin da aka ba shi.

Kungiyar AU ta zabi shugaban Najeriyan ya magance matsalolin lafiya kamar yadda sanarwa ta fito daga Fredrick Nwabufo a shafin X.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a Aso Rock kafin samun kujerar AU Hoto: @Dolusegun16
Asali: Twitter

Mista Fredrick Nwabufo ya fitar da jawabi a yammacin Juma’a da ya yi wa taken ‘An nada Shugaban kasa Tinubu a matsayin gwarzon AU a kan kiwon lafiya.’

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya ki karbar shawarar bude iyakoki da kayyade farashin abinci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Biyo bayan haka, shugaban Najeriyan zai gabatar da jawabi na musamman a wajen taron shugabannin da za a shirya a ranar Asabar.

Mai taimakawa Bola Tinubu wajen hulda da jama'a ya ce kungiyar AU ta yaba ne da irin matakan da gwamnatin tarayya ta dauka.

Daga lokacin da ya shiga ofis, mai bada shawarar ya ce Tinubu ya shirya horas da malaman lafiya 120, 000 a cikin watanni 16 a kasar.

Baya ga haka, gwamnati mai-ci ta dauki damarar nunka dakunan shan magani da ake da su daga 8, 800 zuwa 17, 000 a shekaru uku.

Daga yanzu zuwa 2026, ana kokarin kara yawan asibitocin da ke kananan hukumomi bayan nadin mukamai da aka yi a fannin.

AU: CDC ta nada Bola Tinubu

Hukumar da ke karkashin kungiyar AU wanda ta ke yaki da cututtuka a nahiyar Afrika watau CDC ta sanar da nadin mukamin.

Kara karanta wannan

"Sun rasa muryarsu karkashin Buhari": Shehu Sani ya magantu yayin da sarakunan Arewa ke sukar Tinubu

CDC ta aiko takardar ne zuwa zuwa ma’aikatar harkokin kasashen waje da ke Abuja kuma Tinubu zai yi jawabi a Addis Ababa a gobe.

Sanarwar ta ce hukumar ta shaida an nada Bola Tinubu ne bisa la’akari da shawarar shugabanni da gwamnatocin kasashen Afrika.

Shugabancin kungiyar AU

Shugaban kungiyar AU, Mai girma Azali Assoumani ya amince da nadin mukamin.

A shekarar bara aka nada shugaban kasar Komoros watau Azali Assoumani ya jagoranci AU bayan cikar wa’adin Macky Sall.

Tinubu ba zai bude iyaka ba

An samu labari Bola Ahmed Tinubu ya ki daukar shawarar Kashim Shettima a kan kayyade farashin abinci saboda tsar kaya.

Gwamnatin tarayya ta yi jan-kunne a game da hadarin bude iyakoki domin a shigo da abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng