Tinubu Ya Shiga Sabuwar Matsala Yayin da NLC Ta Ayyana Zanga-Zanga Na Gama Gari, An Yi Karin Bayani

Tinubu Ya Shiga Sabuwar Matsala Yayin da NLC Ta Ayyana Zanga-Zanga Na Gama Gari, An Yi Karin Bayani

  • Kungiyar kwadago ta sanar da cewar za ta yi zanga-zangar gama gari a ranar 27 da 28 ga watan Fabrairu
  • Joe Ajaero, shugaban kungiyar, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a ranar Juma'a a Abuja
  • Ci gaban na zuwa ne kwanaki bayan kungiyar da takwararta ta TUC, sun ba gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu wa'adin kwanaki 14 don tafiya yajin aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ma'aikata karkashin inuwar kungiyar kwadago ta kasa (NLC) sun ayyana zanga-zangar gama gari na kwanaki biyu, wanda za a gudanar a ranar 27 da 28 ga watan Fabrairu.

Shugaban kungiyar, Joe Ajaero, ne ya bayyana hakan a Abuja a ranar Juma'a, 16 ga watan Fabrairu, a wani taron manema labarai da kungiyar ta shirya.

Kara karanta wannan

Auren bogi: EFCC ta maka matashi a kotu kan damfarar masoyiyarsa Ba'amurkiya $373,000

NLC za ta yi zanga-zanga
Tinubu Ya Shiga Sabuwar Matsala Yayin da NLC Ta Ayyana Zanga-Zanga Na Gama Gari, An Yi Karin Bayani Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Joe Ajaero
Asali: Twitter

Yaushe NLC za ta shiga yajin aiki?

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, za a gudanar da zanga-zangar ne domin ganin an cika bukatun 'yan Najeriya kan halin da ake ciki na tsadar rayuwa a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku tuna cewa kungiyoyin NLC da TUC sun bayyana a baya cewa mambobinsu za su fara yajin aiki gama gari nan da kwanaki 14 idan har aka ci gaba da shan wahala a kasar, rahoton Leadership.

Biyo bayan wannan, gwamnatin tarayya ta yi wata ganawa da shugabancin kungiyoyin biyu, inda suka bukaci a dakatar da yajin aikin da ake shirin shiga.

Shin FG za ta hana NLC tafiya yajin aiki?

Tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin karamin ministan kwadago da daukar ma'aikata, Nkeiruka Onyejeocha, sun dauki alkawarin cewa za a dunga biyan albashin kan lokaci daga yanzu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu da gwamnoni sun fara shirin ɗaukar mataki 1 da zai magance matsalar tsaro a Najeriya

Sai dai kuma, Ajaero da mataimakin shugaban TUC, Tommy Okon, sun tsaya kan bakarsu a karshen taron sannan sun bukaci gwamnatin tarayya da ta cika alkawarinta ga ma'aikata.

Ana shirin yajin aiki

A wani labarin, mun ji cewa kungiyar ASUU ta fara nuna cewa batun rashin cika alkawarin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu yana tada mata hankali.

Shugaban kungiyar malaman jami’a na kasa, Emmanuel Osodeke, ya bayyana wannan da kan shi, Punch ta kawo labarin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng