Cross River: Ma’aikatan Gwamnati Sun Fito Zanga-Zaga Kan Wani Dalili 1 Tak, Bidiyo Ya Yadu
- Sabuwar zanga-zaga ta barke a Calabar, babban birnin jihar Cross River, inda ma'aikatan gwamnati ke adawa da rashin biyan su albashi
- Kamar yadda bidiyon zanga-zagar ya yadu, an ga yadda masu zanga-zagar suka mamaye ofishin sakataren gwamnatin jihar
- Masu zanga-zagar sun ce har yanzu da watanni Fabrairu ya raba tsakiya ba a biya su albashi ba, yayin da suke kokawa kan tsadar rayuwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Wasu ma'aikatan gwamnati a jihar Cross River sun fara zanga-zagar nuna bacin rai kan rashin biyan su albashi da har yanzu gwamnatin ba ta yi ba.
Zanga-zagar ta barke ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Fabrairu kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
An nemi masu zanga-zagar su rubuta korafi a hukumance
Ma'aikatan sun yi zuga tare da mamaye ofishin sakataren gwamnatin jihar, Mr. Anthony Owan Enoh.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar masu zanga-zagar, yunwa na yunkurin ganin bayan su yayin da har watan Fabrairu ya raba tsakiya ba a biya su albashi ba.
Sai dai ofishin sakataren gwamnatin jihar ya nemi masu zanga-zagar da su rubuta korafi akan hakan a hukumance.
Bidiyon yadda ma'aikatan suka gudanar da zanga-zangar
Da ya ke wallafa bidiyon yadda zanga-zangar ke gudana, Anthony Ehilebo, wani ma'abocin kafofin watsa labarai ya ce:
"Kai tsaye daga birnin Calabar. Abin da ke faruwa a ofishin sakataren gwamnati kenan. Da alama Najeriya na dab da tarwatsewa. Tattalin arziki ya kara ta'azzara a wannan gwamnati."
Kalli bidiyon yadda zanga-zangar ta gudana:
Fadar shugaban kasa da gwamnonin PDP sun yi musayar yawu
Tun da fari dai gwamnatin Bola Tinubu ta zargi gwamnoni da kara jefa kasar cikin mawuyacin hali ta hanyar kin biyan ma'aikata albashi.
Fadar shugaban kasar ta bayyana hakan a matsayin martani na zarginta da zababbun gwamnonin PDP suka yi na cewar tsare-tsaren Tinubu sun jawo yunwa da tsadar rayuwa.
To sai dai kuma jihar Cross River na karkashin gwamnan APC, Bassey Otu, kuma irin hakan take faruwa na a biya wasu a ki biyan wasu.
Asali: Legit.ng