Abuja: Mota Ta Murkushe Barawo Bayan Fauce Kayan Abincin Wata Mata, Ya Shiga Kakani-Kayi

Abuja: Mota Ta Murkushe Barawo Bayan Fauce Kayan Abincin Wata Mata, Ya Shiga Kakani-Kayi

  • Rana ta baci ga wani barawo yayin da mota ta murkushi a lokacin da ya ke kokarin tserewa da kayan abincin wata mata a Abuja
  • Lamarin wanda ya faru a safiyar Talata a kasuwar Kwali da ke babban birnin, an ruwaito barawon ya samu raunuka da karaya
  • Tun da farko dai matashin ya nemi ya taimaka wa matar wajen daukar kayan zuwa bakin titi, amma ya fakaici ido ya so guduwa da su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Mota ta murkushe wani matashi mai suna Jamilu, a ranar Talata a lokacin da yake yunkurin tserewa da kayan abincin wata mata a kasuwar Kwali da ke a Abuja.

Kara karanta wannan

Kasar Girka ta kuduri aniyar halatta auren jinsi, da daukar rainon yara

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safe inda matashin ya fake da sunan zai taimaka wa matar wajen daukar mata kayan kafin ta samu abin hawa.

Mota ta kade barawon kayan abinci a Abuja
Mota ta kade barawon kayan abinci a Abuja, ya ji raunuka tare da karaya. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Matashin ya yi amfani da salon yaudara

Sun ce matar mai suna Patience Raphael ta gama siyayyar kayan abincin da suka hada da shinkafa, wake, garri, dawa, da dai sauransu, lokacin da ta hadu da matashin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ganau, Ibrahim Audu, ya ce matar tana kokarin samo mai tura baro da zai dauki buhun kayan sai matashin ya nemi ta barshi ya kai mata kayan zuwa bakin titi, rahoton Daily Trust.

Audu ya ci gaba da cewa:

“Ina kokarin kiran wani mai tura baro da zai daukar mata kayan abincin a lokacin da mutumin ya zo ya ce a bari zai dauka.

Kara karanta wannan

Gawa ta ƙi rami: Matar da mijinta ya ayyana cewa ta mutu ta buɗe ido ana dab da ƙona ta

Karo na biyu kenan irin hakan na faruwa a Kwali

Yayin da ya ke kokarin tserewa da kayan da gudu, mota ta kade shi garin tsallaka titi ba tare da waige ba, ya samu raunuka da karaya kuma ’yan banga suka kai shi asibiti."

A baya ma City da Crime sun ruwaito cewa makamancin haka ya faru a makon da ya gabata lokacin da wani mai tura baro ya tsere da buhun shinkafa da sauran kayan abinci na wata mata a kasuwar.

Farashin kayan abinci ya fadi a kasuwar Dawanau, Kano

A wani labarin, kun ji cewa 'yan kasuwa a Dawanau, jihar Kano sun sauke farashin kayan abinci da suka hada da shinkafa, gero, dawa, wake da sauran su.

Wannan na zuwa ne yayin da tsadar rayuwa ke kara ta'azzara a Najeriya, ga kuma rashin ciniki kamar yadda 'yan kasuwar suka bayyana.

Tun bayan dai da gwamnatin Shugaba Tinubu ta janye tallafian fetur tare da karya darajar Naira, tattalin arzikin kasar ya kara durkushewa wanda ya jefa mutane cikin mawuyacin hali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.