Tsadar Rayuwa: Yadda Wani Mutum Ya Dafa Abinci Kan Dutsen Guga Yayin da Farashin Gas Ya Haura N1200

Tsadar Rayuwa: Yadda Wani Mutum Ya Dafa Abinci Kan Dutsen Guga Yayin da Farashin Gas Ya Haura N1200

  • An gano wani mutum cikin bidiyo yana amfani da dutsen guga yana dafa ayaba, yayin da ake siyar da gas kan N1200 kowani kilo a yanzu
  • A bidiyon da aka gano kan TikTok, mutumin ya zuba gawayi cikin dutsen gugan sannan ya daura kwano a kai, kuma sai ga ayaban ya dahu da taimakon garwashin
  • Masu amfani da TikTok da dama sun cika da mamakin abin da mutumin ya yi, sai dai wasu sun ce kwalliya ta biya kudin sabulu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani mutumi da ya yi amfani da dutsen guga wajen dafa ayaba ya yi fice a dandalin soshiyal midiya.

A cikin wani bidiyon TikTok da @adesunkanmi3 ya wallafa, an gano mutumin yana duba ayaban da ya daura a kan dutsen gugan wanda ya dauki zafi.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin da Wani Mummunan Ibtila'i Ya Faru a Hedkwatar APC Ta Ƙasa a Abuja

Tsadar gas ya sa wani mutum girki da dutsen guga
Tsadar Rayuwa: Yadda Wani Mutum Ya Dafa Abinci Kan Dutsen Guga Yayin da Farashin Gas Ya Haura N1200 Hoto: @adesunkanmi3.
Asali: TikTok

Ya yi amfani da dutsen gugan mai amfani da gawayi dauke da garwashi, sannan ya daura kwanon ayaban a kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane sun cika da mamakin cewa ya iya cimma manufarsa bayan ya sha fafutuka wajen girkin.

Sai dai kuma, wasu sun daura alhakin hakan kan tsadar abubuwa kamar su gas din girki, cewa shine dalilin da yasa mutumin ya zabi girki kan dutsen gugan.

A halin da ake ciki, ana siyar da kilon iskar gas kan N1200 a wurare kamar su Port Harcourt.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@DRIZZY ya ce:

"Mutumin da ke shan wahala yana cin ayaban suya?"

@Harper Lewis ya yi martani:

"1kg na gas 1400 ne a yanki na. ya abin yake a yankin ku?"

@Speak ya ce:

"Babu abin da za ku fada mani na yadda wannan mutumin ya taba zuwa Kiri Kiri."

Kara karanta wannan

Tsadar Rayuwa: An bukaci Shugaba Tinubu ya gaggauta yin murabus, karin bayani ya bayyana

@Drey Richie ya yi martani:

"Baaba wannan ya shiga sosai fa."

@dialogwells ta ce:

"Hatta tela ya mayar da kayan aikinsa sun zama na girka abinci. Mutumin bai samu aikin da zai yi da shi ba."

Gwamnatin tarayya za ta raba kayan tallafi

A wani labarin, mun ji cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta raba tallafin kayan hatsi ga talakawan Najeriya, Abubakar Kyari, ministan noma da tsaron abinci ya bayyana.

Kyari ya bayyana hakan ne daga kokarin da gwamnatin Tinubu ke yi na rage yunwa da wahalar da ake sha a kasar, jaridar Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng