Dakarun Sojoji Sun Gano Masana'antar Kera Makamai, Sun Cafke Wanda Ake Zargi
- Rundunar Sojin Najeriya ta kama wasu masu ƙera makamai a jihar Filato a wani samame da ta kai a masana'antarsu
- Wannan farmakin ya samo asali ne sakamakon wajabcin kawar da ayyukan ta'addanci a jihar mai fama da ƴan ta'adda da ƴan bindiga
- Sojojin sun kwato makamai da dama da suka hada da bindigogi ƙirar AK-47 da wasu abubuwa masu haɗari
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Dakarun Operation Safe Haven da ke ƙarƙashin Hakorin Damisa IV sun gano wata ɓoyayyiyar masana'antar ƙera makamai a ƙauyen Pakachi da ke ƙaramar hukumar Mangu a jihar Filato.
Sojojin na gudanar da aikin share fage ne a wani tudu mai cike da tsaunuka a lokacin da suka gano keɓantaccen ginin da ake amfani da shi wajen ƙera muggan makamai.
Sojojin sun kwato tarin makamai da alburusai tare da kama mutum ɗaya da ake zargi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da aka sanya a shafin X na rundunar sojin Najeiya, wanda ake zargin mai suna Mista Tapshak Plangji, mai shekaru 25 da haihuwa, ana kyautata zaton yana da hannu wajen aikata haramtattun ayyuka a masana’antar.
Me sojojin suka ƙwato a masana'antar?
Sojojin na ci gaba da neman wanda ake zargin shi ne mai masana'antar, Mista Nuhu Meshack, wanda ya tsere yayin samamen.
Kayayyakin da aka kwato daga masana'antar sun haɗa bindigogi guda 17, bingiogi AK 47 guda huɗu, ƙananan bindigogi 11 tare da jigida guda biyar, harsasai guda huɗu masu tsawon 0.44, harsasai guda 11 masu kaurin 7.62mm, jigida guda biyar ta AK47.
Sauran kayayyakin sun haɗa da zarto guda uku, bindigogin gida guda 21, guduma guda huɗu, injin yin fenti guda daya, harsasai biyar masu kaurin 9mm da sauran injina masu yawa.
Sojoji Sun Cafke Mace Mai Garkuwa da Mutane
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji a jihar Taraba, sun samu nasarar cafke wata mata wacce ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane.
Sojojin na Bataliya 93 sun cafke matar ne wacce ake zargin lokacin da take ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa na mutumi da aka yi garkuwa da shi.
Asali: Legit.ng