A Karshe, Tinubu Ya Janye Tuhumar da Ake Kan Dan Takarar Shugaban Kasa da Buhari Ya Gurfanar

A Karshe, Tinubu Ya Janye Tuhumar da Ake Kan Dan Takarar Shugaban Kasa da Buhari Ya Gurfanar

  • Yayin da ake zargin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar AAC, a yanzu an wanke shi daga wannan tuhuma da ake yi kansa
  • Ana zargin Omoyole Sowore mamallakin gidan jaridar Sahara Reporters a Najeriya da cin amanar kasa da wasu zarge-zarge da dama
  • Gwamnatin Tarayya ta janye tuhumar ce da ta ke yi na zargin cin amanar kasa a kansa a jiya Laraba 14 ga watan Faburairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta janye tuhumar da ta ke yi wa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar AAC, Omoyole Sowore.

Gwamnatin ta janye tuhumar ce da ta ke yi na zargin cin amanar kasa a kansa a jiya Laraba 14 ga watan Faburairu.

Kara karanta wannan

Babban lamari ya faru bayan mata ta yi ajalin makwabciyarta da wuka kan wani dalili, an rasa ta cewa

Tinubu ya janye tuhumar cin amanar kasa kan dan takarar shugaban kasa
Tinubu Ya Janye Tuhumar Cin Amanar Kasa Kan Sowore. Hoto: Omoyole Sowore.
Asali: Getty Images

Mene ake zargin Sowore da shi?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babbar Kotun Tarayya ta fitar a jiya Laraba 14 ga watan Faburairu, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atoni-janar na Gwamnatin Tarayya, Lateef Fagbemi shi ya mika takardar dakatar da tuhumar kan mamallakin gidan jaridar Sahara Reporters.

Sanarwar ta ce:

"Duba da sashi na 174(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wanda aka yi wa gyaran fuska.
"Ganin ikon da wannan sashi ya bani, ni Lateef Olasunkanmi Fagbemi, SAN na janye wannan tuhuma mai dauke da lamba FHC/ABJ/CR/235/2019."

Tushen laifin da Sowore ya aikata

Sowore wanda ya yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar AAC ya kasance mai yawan kushe da kuma zagin gwamnatin Bola Tinubu kan tsarte-tsarensa.

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari shi ya ba da umarnin gurfanar da Sowore kan zanga-zangar kifar da gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnan Arewa ya sharewa iyalai 70,000 hawaye, ya raba kayan abinci na miliyan 225

Atoni-janar na wancan lokaci, Abubakar Malami shi ya gurfanar da Sowore da Olawale Bakare bayan hukumar DSS ta kama su a watan Agustan 2019.

Daga bisani, DSS ta ki bin umarnin kotu don bai wa Sowore beli inda ake zargin gwamnatin Buhari da take hakkin dan Adam, Premium Times ta tattaro.

Kotu ta dakatar da EFCC tuhumar soja

Kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta dakatar da hukumar EFCC kan tuhumar wani babban soja.

Kotun ta dakatar da Hukumar kan ci gaba da tuhumar Burgediya-janar Nengite Charles kan zargin badakalar kudade.

Ana zargin Nengite da karkatar da makudan kudade lokacin da ya ke kula da hukumar NDDC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.