Wike Ya Sanya Babbar Kyauta Don Cafko Wasu Rikakkun Masu Garkuwa da Mutane a Abuja, Bayanai Sun Fito
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, na son ganin an kawar da masu garkuwa da mutane da suka addabi birnin
- Wike ya sanya tukuicin N20m don cafko wasu riƙaƙƙun masu garkuwa da mutane waɗanda ke da hannu a sace-sace mutane da dama a Abuja
- Ministan ya kuma umurci kwamishinan ƴan sandan Abuja da ya yi duk mai yiwuwa domin ganin birnin ya tsarkaka daga masu aikata laifuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya sanya tukuicin N20m kan wasu riƙaƙƙun masu garkuwa da mutane a birnin tarayya Abuja.
Masu garkuwa da mutanen dai ana zarginsu da hannu wajen kai hari tare da yin garkuwa da wasu jami’an tsaro biyu a wani sansanin sojoji da ke Abuja, cewar rahoton Leadership.
Mutanen biyu, Dahiru Adamu da Abu Ibrahim, ƴan asalin jihar Neja, waɗanda aka fi sani da makiyaya, suna cikin tawagar da ta kashe wani hakimi a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Channels tv ta kawo rahoto cewa Wike ya bayyana hakan ne a lokacin da rundunar ƴan sandan Abuja, take waɗanda ake zargi da aikata laifuka a birnin.
Wane laifi ake zargin masu garkuwa da mutanen?
Suna kuma da hannu a wasu sace-sacen mutane a garuruwan Kabusa, Kutu da sauran ƙauyukan da ke cikin babban birnin tarayya Abuja.
Ministan ya yi gargadin cewa tun da masu aikata laifin sun ƙi barin ƴan Abuja su yi barci, su ma ba za su yi barci ba.
Ministan ya kuma umurci kwamishinan ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja, Oolice, CP Ben Igweh, da ya yi duk mai yiwuwa wajen yaƙar masu laifin.
Tun da farko, kwamishinan ƴan sandan ya bayyana cewa, a ƙoƙarin da suke yi na tsarkake babban birnin kasar daga aikata laifuka, jami’ansu sun kama wasu da ake zargi da aikata laifuka da dama a cikin kwanaki ukun da suka gabata.
Wike Ya Fitar da N30bn Don Yin Wani Aiki a Abuja
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya amince a fitar da N30.9bn don gyaran wasu makarantu a Abuja.
Wike ya amince a kashe N13bn domin gyaran wasu makarantu guda 40 da kashe N13bn wajen sabunta wasu makarantu guda 18, yayin da za a kashe ragowar N4bn ɗin wajen yin wasu ayyuka a makarantu huɗu.
Asali: Legit.ng