Kotu Ta Bada Umarni A Yi Gwanjon Dukiyar Surukin Buhari Saboda Tsohon Bashi

Kotu Ta Bada Umarni A Yi Gwanjon Dukiyar Surukin Buhari Saboda Tsohon Bashi

  • Zargin taurin bashi ya jawo an yi karar Muhammad Sani Sha’aban a kotun musulunci a Zariya
  • Alkali ya karbi korafin da aka gabatar, ya amince a saida kadarorin ‘dan siyasar domin a karbe hakki
  • Kotu ta yarda a sa wasu gine-gine da kamfanonin attajirin saboda ya maidawa abokinsa kudinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Babbar kotun shari’ar musulunci mai zama a unguwar GRA a Zariya, ta bukaci a saida kadarorin Muhammad Sani Sha’aban.

Za ayi gwanjon dukiyar Hon. Muhammad Sani Sha’aban ne domin a iya biyan wani bashin da ya karba, Aminiya ta kawo wannan labari.

Sani Sha'aban
'Danburam Zazzau, tsohon 'dan takaran Gwamna a Kaduna Hoto: Sani Sha'aban
Asali: Facebook

An kai karar Sani Sha'aban kotu

Muhammad Sani Sha’aban ya karbi aron $709,238 da N11, 200, 000 daga hannun abokinsa ne mai suna Alhaji Umar Faruq Abdullahi.

Kara karanta wannan

Hadimin Ganduje yayi tonon asiri, ya nemi Abba ya dawo da Sanusi, a tsige Sarakuna 5

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganin an yi shekaru hudu da karbar bashin ba tare da an biya ba, maganar ta je kotu. Da farko an ce bayan watanni shida za a biya a 2018.

Za a saida kadarorin Sani Sha'aban

Alkalin kotun musuluncin, Ishaq Madahu ya zartar da hukunci a ranar Litinin cewa a nemo wadanda za su saye kadarorin Hon. Sani Sha’aban.

Mai shari’a Ishaq Madahu ya ce idan ba a iya hada duka kudin bayan an yi gwajon kadarorin ba, wanda ake kara zai cika ragowar kudin.

A yayin da dukiyar da aka saida ta zarce bashin da ake bin ‘dan siyasar, za ayi masa ciko.

Wani sharadi da kotun shari’ar ta bada shi ne za a biya bashin yadda aka karba, watau za a nemo Dala ba tare da la’akari da farashi ba.

Lauyoyin Sani Sha'aban da Umar Faruq Abdullahi

Kara karanta wannan

NNPP ta yadu zuwa wajen Kano, Jam’iyya Ta Samu ‘Dan Majalisa a Jihar Nasarawa

Jaridar ta rahoto lauyan da ya shigar da kara, Kabir Momoh yana cewa sun gamsu da hukuncin da alkali ya yi, ya ce an yi masu adalci.

Da aka nemi jin ta bakin lauyan wanda aka yi kara, ya nuna ba zai ce uffan game da shari’ar ba domin bai samu izinin yin magana ba.

Kadarorin da za a saida a kasuwa

A cikin kadarorin da aka dogara da su wajen cin bashin akwai wani gini a Bompai Kano da Kamfanin Mazari Ltd da yake jihar Kaduna.

Haka akwai shagon Tulips wanda Legit ta fahimci yana kusa da asibitin Al-Madina a Zariya da wani gini kusa gidansa duk a unguwar GRA.

Takarar Sani Sha'aban a 2023

A bara ne aka ji labari tsohon abokin tafiyar Muhammadu Buhari a ANPP kuma surukinsa, ya sha alwashin kifar da APC a Kaduna.

Muhammad Sani Sha’aban ya fito yin takarar Gwamna a jam'iyyar ADC, sai dai bai yi nasara ba domin Uba Sani ya doke shi a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng