Kano: Kotu Ta Sake Daukar Muhimmin Mataki Kan Abba Kabir Game da Rusau, Ta Bayyana Dalilai
- Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kano ta yi hukunci kan rusau da ake ci gaba da yi a jihar Kano
- Kotun ta haramtawa Gwamna Abba Kabir na jihar kan shirin rushe gidaje a Unguwar Salanta da ke birnin
- Gwamnan ya sakawa wasu gidaje jan layi don rushe su inda ya ke zargin ba a gina su bisa ka'ida ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta haramtawa Gwamna Abba Kabir rusa wasu gidaje.
Kotun wacce ta yi hukuncin a yau Talata 13 ga watan Faburairu ta haramtawa gwamnan rushe gidajen ne a Unguwar Salanta.
Wane hukunci kotun ta yanke?
Gwamnan ya gindaya wasu gine-gine tare da saka musu jan layi don rushe su inda ya ke zargin ba a gina su bisa ka'ida ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mazauna Unguwar da abin ya shafa sun garzaya kotu don neman hakkinsu a gabanta.
Daily Trust ta tattaro cewa Mai Shari'a, Simon Amobeda ya tabbatar da cewa gidajen da aka gina an same su da hanyar da ta dace.
Har ila yau, ya ce babu yadda za a yi a rushe su ba tare da sanin mamallakan wuraren ba, Legit ta tattaro.
Mafarin rusau a Kano
Kokarin jin ta bakin kwamishinan Shari'a a jihar, Haruna Dederi ya ci tura don jin wani irin mataki gwamnatin za ta dauka a gaba.
Tun farkon hawan Gwamna Abba Kabir karagar mulki yake rusau da ya ke zargin an gina su ba bsa ka'ida ba.
A dalilin haka, kungiyar 'yan kasuwa ta maka shi a kotu kan rushe musu shaguna inda kotu ta bukaci ya biya su diyyar biliyan 30.
Abba Kabir ya bukaci rahoto daga kwamishinoni
Kun ji cewa, Gwamna Abba Kabir ya umarci kwamishinoni a jihar su rubuto ayyukansu cikin watanni da suka gudanar.
Gwamnan ya ba su wa'adin kwanaki 10 da su rubuto rahoton don sanin kokarin kowa da yanke hukunci a kansa.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya cika watanni takwas kenan a kan karagar mulki tun bayan rantsuwa a watan Mayun 2023.
Asali: Legit.ng