Kano: Kotu Ta Yi Hukunci a Shari'ar da Mawaki Ya Maka BBC Hausa a Kotu, Bayanai Sun Fito

Kano: Kotu Ta Yi Hukunci a Shari'ar da Mawaki Ya Maka BBC Hausa a Kotu, Bayanai Sun Fito

  • Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan karar mawaki a Kano da ya maka BBC Hausa kan satar fasaha
  • Yayin hukuncin, kotun ta ki amincewa da bukatar mawaki, Abdul Kamal kan dakatar da BBC daga amfani da kidansa
  • Wannan na zuwa ne bayan mawaki a Kano, Abdul Kamal ya maka BBC Hausa kan amfani da wakarsa ba tare da izini ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano ta ki amincewa da bukatar mawaki, Abdul Kamal kan dakatar da BBC Hausa daga amfani da kidansa.

Mai Shari'a, Muhammad Nasir Yunusa shi ya yi hukuncin a yau Litinin 12 ga watan Faburairu a birnin Kano.

Kara karanta wannan

An ji kunya: Matasa masu karfi a jika sun kashe zuciyarsu, sun sace fanka a masallaci

Kotu ta yi hukunci kan karar BBC Hausa d mawaki ya yi a Kano
Kotu ta ki amincewa da bukatar mawaki Kamal Kan BBC Hausa. Hoto: BBC Hausa.
Asali: Facebook

Mene ake zargin BBC Hausa da aikatawa?

Wannan na zuwa ne bayan wani mawaki a Kano, Abdul Kamal ya kai karar BBC Hausa kan amfani da wakarsa a shirin “Daga Bakin Mai ita” ba tare da izini ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta ce tun da ita ke da hurumin hanawa ki ba da damar amfani da kidan, ta yi fatali da karar saboda rashin hujjoji.

Alkalin kotun ya bukaci bangarorin da ke shari’ar da su tabbatar da martani kafin dage shari’ar zuwa ranar 20 ga Maris, cewar Daily Trust.

Martanin dukkan lauyoyin bangarorin guda biyu

Barista Shakiruddeen Mobuluwaji wanda shi ne lauyan BBC Hausa ya ce har zuwa yanzu lauyan mai kara bai yi martani ga karar da suka daukaka ba.

Sai dai lauyan mai kara, Barista Bashir Ibrahim ya bayyana cewa tuni suka mayar da martani ga lauyoyin wadanda ake kara, cewar Quest Times.

Kara karanta wannan

Gasar AFCON: An shiga karancin rigunan Super Eagles a Kano, 'yan kwasuwa sun kwashi ganima

Daga karshe, Alkalin kotun ya bukaci dukkan bangarorin da su tabbatar da martanin kafin ranar 20 ga watan Maris da za a ci gaba da shari'ar.

Kamal ya maka BBC Hausa a kotu

A baya, kun ji cewa wani matashin mawaki a Kano, Abdul Kamal ya maka BBC Hausa kan satar fasaha na wata daga cikin kidansa.

Kamal na zargin BBC Hausa da yin amfani da kidansa a shirinsu ba tare da neman izninsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel