Innalillahi: Mahara Sun Hallaka Jami'an ’Yan Sanda 2 da Sace Fiye da 40 a Sabon Hari a Zamfara
- An shiga tashin hankali bayan ‘yan bindiga sun hallaka jami’an ‘yan sanda biyu tare da sace mutane 40 a harin
- Lamarin ya faru ne da safiyar yau Talata 13 ga watan Faburairu a kauyen Kasuwar-Daji a karamar hukumar Kaura Namoda
- Legit Hausa ta ji ta bakin wani mazaunin garin Kasuwar-Daji inda ya tabbatar da faruwar lamarin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Wasu ‘yan bindiga sun hallaka jami’an 'yan sanda biyu da sace wasu mutane 40 a jihar Zamfara.
Harin ya faru ne a kauyen Kasuwa Daji a karamar hukumar Kaura Namoda da ke jihar.
Yaushe aka kai harin a Zamfara?
Mazauna yankin sun tabbatar da cewa maharan sun durfafi kauyen ne da safiyar yau Talata 13 ga watan Faburairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Channels TV ta tabbatar da cewa maharan na dauke da muggan makamai hade da makamin kakkabo jirgin sama.
Majiyar ta ce maharan sun kuma kai hari gidan tsohon shugaban kungiyar NURTW, Hamisu Kasuwar-Daji inda suka sace matarsa da jikokinsa.
An tabbatar da cewa gidan Hamisu na kusa da ofishin ‘yan sanda inda suka farmaki ofishin tare da hallaka jami’ai biyu da dauke makamansu.
Har ila yau, wani mazaunin yankin da ya bukaci a boye sunansa ya ce maharan sun kuma hallaka wasu mutane biyu yayin kai harin, cewar Politics Today.
Ya tabbatar da cewa akalla mutane 40 aka sace yayin kai harin da maharan suka yi gida-gida.
Legit Hausa ta ji ta bakin wani mazaunin garin Kasuwar-Daji, Mustapha Kasuwar-Daji kan harin.
Mustapha ya ce tabbas karfe daya na dare suka ji ana ta harbe-harbe inda aka kashe 'yan sanda biyu da farar hula daya.
Ya ce:
"Cikin dare misalin karfe daya muka ji ana ta bude wuta inda aka kashe jami'an 'yan sanda biyu da farar hula daya.
"Sannan an harbi wani farar hula daya inda yanzu haka ya na asibiti don karbar kulawa, har ila yau an sace mutane da dama."
Martanin 'yan sanda kan harin
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Abubakar Yazid ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai bai bayyana adadin mutanen ba.
Ya ce:
“Tabbas an kai hari a Kasuwar-Daji da safiyar yau, har yanzu bamu tabbatar da yawan mutanen da abin ya shafa ba.”
‘Yan daba sun farmaki kwamishina a Adamawa
Kun ji cewa, wasu ‘yan daba sun kai farmaki gidan kwamishinan Muhalli, Mohammed Sadiq a jihar Adamawa.
Sadiq ya gamu da tsautsayin ne a daren ranar Lahadi 11 ga watan Faburairu inda ya samu raunuka da dama.
Asali: Legit.ng