Hukumar IMF Ta Bai Wa Tinubu Shawara Kan Cire Tallafin Mai da Wutar Lantarki, Ta Fadi Dalilai
- Hukumar IMF ta yi magana kan muhimmancin cire tallafin mai gaba daya da kuma tabbatar da cire na wutar lantarki
- Hukumar ta shawarci gwamnatin da cewa ya kamata ta cire dukkan tallafin saboda yawan kudade da ta ke kashewa
- Ta ce tallafin mai da wutar lantarki su na cin kudade sosai kuma ba su isa inda ya kamata ga talakawa wadanda aka yi don su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar Ba Da Lamuni Ta Duniya (IMF) ta bai wa gwamnatin Najeriya shawara kan cire tallafin mai da wutar lantarki a kasar.
Hukumar ta ce ya kamata gwamnatin Najeriya ta cire dukkan tallafin saboda yawan kudade da ta ke kashewa.
Mene Hukumar IMF ke cewa ga Tinubu?
Ta ba da shawarar ce a wani rahoto da ta fitar inda ta ce hakan ne kawai zai bunkasa tattalin arzikin kasar, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta koka yadda Tinubu ta fitar da kayan abinci a Baitul Mali da kuma ba da takin zamani mai sauki ga jama'ar kasar.
IMF ta ce wwadanan matakai da ta dauka ya mayar da cire tallafin mai din da ta yi a baya ta wata hanya daban wanda hakan koma baya ne.
Shawarin da IMF ta bai wa Tinubu
Sannan ta bukaci Shugaba Tinubu ta cire tallafin mai da wutar lantarki gaba daya inda ta ce tallafin ba ya isa ga talaka, New Telegraph ta tattaro.
A cewar sanarwar:
"Sabuwar gwamnatin ta dauki matakai masu karfi da za su dakile matsalolinta kasar.
"Tallafin mai da wutar lantarki su na cin kudade sosai kuma ba su isa inda ya kamata ga talakawa.
"Tun da bukatar su isa ga wadanda suka fi bukata ne, kuma ba a samun haka, ya kamata a cire su gaba daya."
Ministan Tinubu ya fadi amfanin cire tallafi
Kun ji cewa, Ministan yada labarai a Najeriya, Mohammed Idris ya fadi amfanin cire tallafin mai a kasar da Shugaba Tinubu ya yi.
Idris ya ce da kudaden da ake samu bayan tallafin ake samun damar gudanar da wasu ayyuka na musamman a kasar.
Asali: Legit.ng