Mun Gaji da Jira: Ma’aikatan Tarayya Sun Fusata, Har Yanzu Ba Su Sami Albashin Janairu Ba

Mun Gaji da Jira: Ma’aikatan Tarayya Sun Fusata, Har Yanzu Ba Su Sami Albashin Janairu Ba

  • Har yanzu da muke a rana ta 12 cikin watan Fabrairu, akwai ma'aikatan tarayyar da ba su sami albashin su na watan Janairu ba
  • Akalla ma'aikatu da hukumomin tarayya 90 ne ma'aikatan su ba su sami albashin ba da suka hada da ma'aikatar ilimi, hukumar kidaya
  • A cikin hirarraki daban-daban, ma’aikatan sun koka da yadda suka ce bai kamata a maimaita jinkirin albashinsu na Disamba 2023 ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ma’aikatan gwamnatin tarayya a ma’aikatu da hukumomi kusan 90 har yanzu ba su samu albashin watan Janairu ba.

Ma'aikatun da abin ya shafa sun hada da ofishin shugaban ma’aikatan tarayya (OHoCSF), da ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a ta kasa.

Kara karanta wannan

Kogi: An tsinci gawar daliban kwaleji a dakin kwanansu, an gano abin da ya kashe su

Ma'aikatan tarayya sun fusata akan rashin samun albashin Janairu
Ma'aikatan tarayya sun fusata akan rashin samun albashin Janairu
Asali: UGC

Ma'aikata sun koka da jinkirin biyan albashi

Sauran ma'aikatun sun hada da ma’aikatar ilimi, hukumar kidaya ta kasa, kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), muryar Najeriya da sauran su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin hirarraki daban-daban da Daily Trust da Premium Times, ma’aikatan sun koka da yadda suka ce bai kamata a maimaita jinkirin albashinsu na Disamba 2023 ba.

Daya daga cikin ma'aikatan yace:

“Yayin da nake magana da ku, ba a biya ni da abokan aikina guda uku ba. Hakan bai dace ba idan aka yi la’akari da halin da ake ciki na hauhawar farashin kayayyakin abinci."

Dalilin jinkirin biyan albashin Disamba da Janairu

Wasu kuma sun yi zargin cewa jinkirin biyan albashin na su wata alama ce da ke nuna cewa gwamnati ba ta damu da irin wahalhalun da talakawa ke ciki ba.

Kara karanta wannan

EFCC ta tsitsiye kanin tsohon ministan Buhari kan badakalar naira biliyan 8

An danganta jinkirin biyan albashin watan Disamba ga al'amuran fasaha da suka shafi lodawa da daidaita 'tsarin biyan albashin bai daya da bayanan ma'aikata (IPPIS).'

An daura alhakin jinkirin biyan albashin watan Janairu a kan matsalar fasaha da aka samu a tsarin hada-hadar kudi na gwamnati (GIFMIS) da ke karkashin ofishin Akanta-Janar na Tarayya (OAGF).

An nemi gwamnati ta dauki matakin gaggawa

Wani jami’in jami’ar tarayya, Oye Ekiti, Wole Balogun, ya ce lura da irin wahalhalun da jama’a ke fuskanta, bai kamata ayi jinkirin biyan albashi ba.

Balogun, wanda ya dora alhakin jinkirin da aka samu a kan wani cikas na tsarin mulki da ya shafi tsarin biyan kudi, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki kan biyan bashin, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

An kaddamar da kwamitin karin albashi

Tun da fari, Legit ta ruwaito maku cewa, mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima, ya kaddamar wani kwamitin mutum 36 da zai duba batun karawa ma'aikata albashi.

Kara karanta wannan

Yadda jami’an yan sanda suka yi garkuwa da wani mazaunin Abuja, suka kwashe gaba daya kudin asusunsa

Gwamnati ta fara shirye-shiryen karin albashin ne bayan da tattalin arzikin kasar ya durkushe yayin da aka samu hauhawar farashin kayan masarufi da ya haddasa tsadar rayuwa.

Ana sa ran kwamitin zai ba gwamnati shawara kan sabon mafi karancin albashin da ya kamata a rinka biyan ma'aikata a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.