"Ya Kamata a Yiwa ’Yan Najeriya Ka’ida Wajen Hawa Shafukan Sada Zumunta", Gwamnan Ekiti Ya Tono Batu
- Gwamnan jihar Ekiti ya bayyana bukatar a kawo sauyi ga yadda ake amfani da kafafen sada zumunta musammam ma a Najeriya
- Najeriya na daga kasashen da kowa ke fadin abin da ya ga dama a kafar sada zumunta ba tare da daukar mataki kan lokaci ba
- Ya bayyana ta yadda hakan zai taimaka wajen kawo ci gaba da wanzuwar ababen alheri ga kasar mai dimbin matasa da ke amfani da yanar gizo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Jihar Ekiti - Gwamnan jihar Ekiti, Peter Ayodele Fayose ya bayyana tsananin bukatar a yiwa amfani da kafafen sada zumunta ka’ida a Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani rubutun da ya yada a kafar Twitter, inda yace rashin hakan barazana ce babba ga Najeriya.
A cewar gwamnan, tabbas kafafen sada zumunta na da amfani, amma barin sakaka babu wata kula ka iya jefa kasar nan ga hadari nan gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meye kawo ka’ida ga kafafen sada zumunta zai kawo?
Ya kuma yi tsikaci da cewa, samar da ka’idojin zai taimaka wajen tabbatar da amfana da kafafen ta hanyoyin da suka dace kwarai.
A kalamansa, gwamnan ya ce:
“Gaskiyar da ya kamata mu fuskanta ita ce ba zai yiwu mu ci gaba da amfani da kafafen sada zumunta babu ka’ida ba. Dole ne a tsara ka’idojin amfani da shi daidai da doka ga masu dandamali da masu amfani dashi.
“Babu shakka kafofin sada zumunta sun zama masu mahimmanci ga wanzuwarmu, amma dole ne a sami ka'idojin da ke jagorantar amfani da shi.”
A duniya ana yin ka’ida ga amfani da kafafen sada zumunta?
Da yake karin haske game da halin da duniya ke ciki, gwamnan ya ce:
“A duk duniya, kafafen sada zumunta na taka rawar gani wajen yaki da laifuka kuma Najeriya ba ta bar baya ba.
“Sai dai, yana da kyau kamar yadda kafafen sada zumunta suke, matakin cin zarafi da amfani da shi wajen yada rsahin fahimta abin damuwa ne. Babu wata al'umma ko gwamnati mai hankali da za ta nade hannunta akan wadannan wuce gona da iri. Ana a wasu kasashe.
“Duk da cewa al'ada ce 'yan Najeriya su yi shakkun dokokin gwamnati, amma masu amfani kafafen sada zumunta da kyakkyawar niyya ba su da wani abin da su ji tsoro.”
An taba hana Twitter a Najeriya
Idan baku manta ba, an taba haramta amfani da manhajar Twitter a Najeriya, duba da wasu dalilai na barazanar sakin bayanai sakaka a kafar.
Wannan lamari ya dauki hankali ainun, amma an bayyana asarar da Najeriya ta tafka ta dalilin daukar matakin hanin nan take.
A wancan lokacin, an samu sulhu tsakanin Najeriya da kamfanin mai yawan matasa da jami’an gwamnati da ma hukumomi.
Asali: Legit.ng