Gwamnatin Najeriya ta bayyana inda aka kwana a kan dakatar da Twitter da zaman sulhu

Gwamnatin Najeriya ta bayyana inda aka kwana a kan dakatar da Twitter da zaman sulhu

  • Tun a farkon Yuni aka dakatar da kamfanin Twitter daga aiki a Najeriya
  • Hadimin Ministan shari’a ya ce kwamitin sulhu bai zauna da kamfanin ba
  • Ana sa ran ba da dadewa ne bangarorin biyu za su zauna domin ayi sulhu

Gwamnatin tarayya ta ce kawo yanzu, ba ta soma yin zama domin ayi sulhu da kamfanin Twitter da aka dakatar da aikinta tun a watan Yunin da ya wuce ba.

An hana Twitter aiki a Najeriya

A ranar 4 ga watan Yuni, 2021, gwamnatin tarayya ta bada sanarwar hana Twitter aiki a Najeriya, hakan na zuwa ne bayan sun goge maganar shugaban kasa.

Makonni uku kenan da daukar wannan mataki na hana kamfanin Twitter aiki a Najeriya, amma kwamitin da shugaban kasa ya kafa bai soma aiki ba tukuna.

KU KARANTA: Dakatar da Twitter a Najeriya zai kawo cikas - Yan kasuwa

Punch ta ce zuwa yanzu ko sau daya wakilan gwamnatin tarayya ba su zauna da bangaren Twitter domin a samu maslaha tsakanin bangarorin biyu ba.

Kwamitin da shugaban kasa ya kafa

Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Alhaji Lai Mohammed shi ne shugaban kwamitin da ke kunshe da Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami da Geoffrey Onyema.

Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Babatunde Fashola SAN, Festus Keyamo SAN, da Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnati Abubakar Malami SAN.

Mai magana da yawun bakin Ministan shari’a na kasa, Dr. Umar Gwandu ya ce an kammala shirin yadda wannan kwamiti zai zauna da wakilan kamfanin.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari Hoto: www.guardian.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Twitter ta yi martani bayan dakatar da ita a Najeriya

“Ba a soma zaman sulhun ba tukuna. Shirin sulhun ya fara ne da kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa.”
“Ana shirin sasanta wa. Jama’a za su san halin da ake ciki ta bakin ‘yan jarida a lokacin da aka cin ma matsaya.”

Jaridar ta yi kokarin ta tuntubi Twitter a kan lamarin, amma har yanzu ba su iya cewa komai.

A makon yau aka ji cewa shugaba Muhammadu Buhari ya zabi wanda zai wakilci mutanen Najeriya a kujerar kungiyar kasuwanci na Duniya watau WTO.

Dr. Adamu Mohammed Abdulhamid ya zama sabon Jakadan Gwamnatin Tarayya a WTO.

Asali: Legit.ng

Online view pixel