Ku kirkiri taku kafar: APC ta kalubalanci matasan Najeriya bayan hana Twitter

Ku kirkiri taku kafar: APC ta kalubalanci matasan Najeriya bayan hana Twitter

- Jam'iyyar APC ta bukaci matasan Najeriya da su kirkiro kafar sada zumunta kamar Twitter a kasar

- Jam'iyyar ta yi wannan kiran ne bayan da gwamnatin kasar ta dakatar da ayyukan kamfanin Twitter

- APC ta bayyana imanin da cewa na Najeriya na da matasa masu gwazon da za su iya aiki don samar da wata kafa

Jam’iyyar APC ta bukaci ‘yan Najeriya wadanda suka kware wajen kirkirar kafofin sada zumunta/manhajoji da su zo da manhajojin sada zumunta na kasar.

Jam’iyyar mai mulki ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren rikon ta na kasa, Sen. John James Akpanudoedehe, kuma ta gabatar wa Legit.ng a ranar Asabar, 5 ga watan Yuni.

Legit.ng ta lura cewa bayanin na APC ya biyo bayan shawarin gwamnatin tarayya na dakatar da ayyukan Twitter a Najeriya.

KU KARANTA: Bukola Saraki Da Atiku Sun Yi Martani Kan Dakatar Da Kafar Sada Zumuta Ta Twitter

Ku kirkiri taku kafar: APC ta shawarci matasan Najeriya bayan dakatar da Twitter
Ku kirkiri taku kafar: APC ta shawarci matasan Najeriya bayan dakatar da Twitter Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Jam'iyyar mai mulki ta lura cewa kasashe kamar Rasha da China suna da nasu dandalin sada zumunta.

Wani bangaren sanarwar na cewa:

"Jam'iyyar APC ta yi imanin cewa kasar na da masu karfi da baiwa wadanda za su iya samar da wasu dandamali da za su yi gasa da wadanda da ake da su a duniya.
"Tabbatar da dakatarwar ta Twitter zai kasance aiki ne na kwarai don fito da kwarewar 'yan Najeriya a fagen fasaha a duniya.
"Wannan kalubale ne ga matasanmu masu kwazo da irin wannan baiwa. Za su samu goyon baya a wannan aiki daga hukumomin gwamnatin tarayya da suka dace da kuma horaswa a hanyoyin fasahar sadarwa ta ICT da cibiyoyin bincike a kasar."

KU KARANTA: NCC Ta Ba Kamfanonin Sadarwa Umarnin Hana ’Yan Najeriya Damar Hawa Twitter

Legit ta ji ta bakin wasu matasa kan wannan kalubale na APC, yayinda wasu suka ce lallai akwai gaskiya ciki, wasu sin caccaki jam'iyyar.

Bahr Sabar yace: "Kai amma na ji dadin wannan qalubalen. Kamata ya yi a basu tallafin duk abinda suke da bukata domin yin hakan. Idan ya so sai a maida ita mallakar gwamnati.

Ku tashi tsaye matasa, wannan qalubalen bai fi qarfinku ba."

Mujaheed Ya'u Umar yace: "Aikin banxa kai..Kuma ai duk rashin kwarewar ne ya kuka gudu daga #field_of_study naku kuka tafi siyasa saboda nan ne gidan mahaukata,ko wanne jaki da kare sai a riskeshi anan."

Augustine G Augustine yace: "Ai mastalar shi ne rashin iya Kama ludayin mulkinku ne shiyasa, inbahakaba ai matasan Nigeria suna da basiran yin haka Amma basa samun tallafi daga wurin gwabnati."

A wani labarin, Fadar shugaban kasa ta bayyana dakatar da Twitter a Najeriya a matsayin na dan wani lokaci, inda ta ba da alamun cewa nan ba da jimawa ba ‘yan Najeriya za su samu samu damar sake shiga kafar ta yanar gizo.

Legit.ng ta lura cewa wannan bayanin yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, 5 ga watan Yuni.

Yayin da yake karin haske kan dalilin da ya sa aka dakatar da Twitter, Shehu ya bayyana matakin gwamnatin a matsayin "na wani lokaci".

Asali: Legit.ng

Online view pixel