Arziki Mai Rana: Yadda Matashi Ya Siya Abincin Mai Talla Gaba Daya, Ya Rabawa Marasa Galihu

Arziki Mai Rana: Yadda Matashi Ya Siya Abincin Mai Talla Gaba Daya, Ya Rabawa Marasa Galihu

  • Wani dan Najeriya mai suna Osita Obidike ya saukaka rayuwar wata mata mai siyar da abinci ta hanyar siye komai tare da rabawa mabukata
  • Kafin ya yi mata wannan karimcin, mutumin ya ganta ne tana barci a kan kujera tana jiran kwastomomi su zo su siya abincin
  • ‘Yan Najeriya da dama sun yaba masa da yadda ya yi amfani da kudinsa wajen kyautatawa da kuma ciyar da marasa galihu a kan titi

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Shahararren dan TikTok, Osita Obidike (@ositapopcorn), ya sanya murmushi a fuskar wata mata ‘yar kasuwa a lokacin da ba ta yi tsammanin hakan ba.

Kara karanta wannan

Shahararren malamin addini ya tona asirin malaman da ke kara rashin tsaro a kasar, ya ba da shawara

Osita ya ga matar ne tana kishingide a rumfar siyar da abinci saboda babu kwastoman da ya zo siya, inda ya matso kusa da ita ya mata magana kan abin da take siyarwa.

Yadda matashi ya taimaki talakawa da abinci
Ana tsadar abinci, matashi ya taimaki jama'a | Hoto: @ositapopcorn
Asali: TikTok

Dafaffiyar shinkafa kyauta ga mabukata

Matashin ya ce a shirye yake ya siya duk wani abu da take sayarwa, sai ta ce masa komai da komai na abin da take siyarwa idan aka hada N30,000 ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka nan ya yarda, ya nemi ta taimaka masa ya raba abincin ga wadanda ke bukata a bakin titi.

Bayan ya gama aikin rabon, sai ya saka mata albarka da tare da ba ta kudinta kamar yadda suka yi alkawari. Matar ta durkusa ta gode ya yi wucewarsa.

Kalli bidiyon abin da ya faru a nan:

Martanin jama’a a kafar sada zumunta

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ta yiwu Tinubu ya rufe iyakar Najeriya kan karancin abinci, ya fadi sauran hanyoyi

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kafar sada zumunta, ga kadan daga abin da wasu ke cewa kan abin da matashin ya aikata:

YOGA RICHIES ya ce:

"Allah ya hana aljihunka bushewa."

Shomes ya ce:

"Gaskiya bata da hali mai kyau ko kadan."

Adedoyin ya ce:

"Ba mamaki ban ganta a shago ba. Kenan kai ka siye abincin da nake siya."

Boy Alone ya ce:

"Daya daga cikin dalilan da yasa nake son zama mai arziki."

chidinma tace:

"Tabbas ta farka da wuri don girkin, wannan abu yayi kyau. Allah ya saka da alkhairi malam."

VIKKOOFFICIAL ya ce:

"An kammala kasuwanci a mintuna 20 maimakon kamar kwana 5, Allah ya albarkace ka da ciyar da marasa galihu."

ab_boogie ya ce:

"Wata rana zan yi wannan na rantse."

MEL ky ya ce:

"Idan da kudi kasar nan da babu wanda zai je ofishin jakadanci ya nemi visa."

Kara karanta wannan

Hanya 1 tak da gwamnatin tarayya ta dauka don karya farashin kayan abinci, Ministan Yada Labarai

#hollow yace:

"A gaskiya 'yan Najeriya mutanen kirki ne, kawai takaici ne ya yi yawa a kasarmu a zahiri."

Martanin Kwankwaso kan tsadar abinci

A wani labarin kuma, jigon jam’iyyar APC a jihar Kano, Ilyasu Musa Kwankwaso ya yabawa matakin fitar da abinci da Shugaba Tinubu ya yi.

Kwankwaso wanda tsohon kwamishina ne a jihar ya ce fitar da tan dubu 102 na kayan abinci zai taimaka wurin dakile tsadar abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.