Talaka Zai Sake Shiga Kunci, Farashin Man Jirgin Sama Ya Karu, an Kara Kudin Sufuri a Najeriya
- Jiragen saman da ke aiki a Najeriya sun kara kudin sufuri biyo bayan karin da aka samu a farashin makamashi na jirgin sama
- Kamfanonin sufurin jiragen sama sun yi korafi da cewa, akwai batutuwan da suka jawo karin, ciki har da rashin daidaito a musayar kudade
- Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da man jirgin sama ya koma 1,300 a kowacce lita, wanda a baya bai kai haka ba
Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Kamfanonin sufuri a Najeriya sun dauki matakin kara kudin sufuri biyo bayan karin da aka samu na farashin man jirgi da ya haura zuwa N1,300 a kowacce lita.
Obiora Okonkwo, mai magana da yawun kamfanonin jiragen sama a Najeriya ne ya bayyana hakan, inda ya bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta kawo dauki a fannin sufurin jiragen sama.
Meye ya jawo karin kudin hawa jirgi a Najeriya?
Kamfanonin jiragen sun yi korafin cewa, rashin daidaito da tabbas a kasuwannin musayar kudi da kuma karuwar farashin makamashi ne ke kan gaba wajen karuwar kudin sufurin jirage.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya koka da cewa, a halin yanzu ana siyar da litar man jirgi a kan farashin N1,300, lamarin da ya jawo tsaiko ga ci gaban fannin sufurin jiragen sama, Punch ta ruwaito.
Ba fannin man jirgi ba, kusan kowanne bangare a Najeriya na fama da tsada biyo bayan yadda Naira ke karyewa a kasuwar duniya.
Nawa ake musayar Naira zuwa Dala?
A halin da ake ciki, darajar Naira ta fadi kasa warwas, inda ake musanyata da Dala a kan N1,500 a kasuwa bayan fage, N1,474 a halastacciyar kasuwa, TechEconomy ta tattaro.
Wannan babbar barazana ce, domin ‘yan Najeriya da dama na kukan yadda abubuwa suka yi tashin goron zabi a kasar.
Kusan karin kaso 50% ake samu kan wasu daga cikin kayayyakin da ake siya don amfanin yau da kullum a Najeriya tun bayan karyewar kudin.
'Yan kasuwar canji a Abuja sun rufe shaguna
A wani labarin, 'yan kasuwar canji (BDC) sun sanar da dakatar da aiki a Abuja sakamakon rashin samun wadatattun takardun dalar Amurka.
Shugaban kungiyar 'yan kasuwar, Mallam Abdulahi Dauran ne ya sanar da hakan a babban birnin kasar a ranar Laraba.
Asali: Legit.ng