Kperogi Ya Fadi Abin da Zai Faru Idan Tinubu Ya Gaza Shawo Kan Tsadar Rayuwa a Najeriya
- Farfesa Farooq Kperogi, ya bukaci Shugaban kasa Bola Tinubu da ya kula da zanga-zangar da ake yi kan tsadar rayuwa
- A wani rubutu da ya wallafa, Farfesa Kperogi ya ce idan ba a magance lamarin ba, za a gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan da 'dan lokaci
- Jaridar Legit ta rahoto cewa Kperogi ya bukaci Shugaban kasa Tinubu da ya daina yin abubuwa kamar magabacinsa, Muhammadu Buhari
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Wani shahararren marbuci, Farfesa Farooq Kperogi, ya gargadi Shugaban kasa Bola Tinubu cewa "hauhawan farashin kaya da ke faruwa a Najeriya ba bisa ka'ida ba" babban barazana ne ga zamantakewar kasar.
Kperogi ya ce zanga-zangar da ya gudana a jihohin Neja, Kano da Osun a baya-bayan nan, alamun gargadi ne ga gwamnatin Tinubu.
Me Kperogi yake hangowa Tinubu?
A rubutunsa da ya yi na mako, Kperogi ya yi gargadin cewa idan har manufofinsa (Tinubu) na rashin tausayi ya haifar da bore na gama gari, yankin Kudu maso Yamma ba zai zame masa kariya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marubucin ya bayyana cewa mafita guda akan abin da ya bayyana a matsayin 'hatsari' shine Shugaban kasa Tinubu ya bayar da shugabanci nagari da tausayi.
Kperogi ya rubuta:
"Sakin dubban Metric Tan na hatsi mataki ne mai kyau na farko, amma ko kusa bai isa ya dakatar da tarzomar da ta barke a kasar ba. Iyakar abin da zai yi, shine zai jinkirta abin ne kawai."
Jaridar Legit ta rahoto cewa dubban 'yan Najeriya a garin Minna, babban birnin jihar Neja, sun gudanar da zanga-zanga a kwanan nan kan abin da suka bayyana a matsayin tsadar rayuwa.
An gudanar da zanga-zanga makamancin wannan a jihohin Kano, Filato da Kogi.
Ana ci gaba da zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya
A halin da ake ciki, Legit Hausa ta rahoto cewa al’ummar Legas sun bi sahun jihohin da aka gudanar da zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da tsadar rayuwa a ƙasar nan.
A Legas, mata da matasa ƴan kasuwa sun yi zanga-zanga a unguwar Ibeju-Lekki da ke jihar Legas a ranar Asabar, 10 ga watan Fabrairu.
Asali: Legit.ng