Sarkin Musulmi da Kiristoci Sun Hada Kai, Sun Taso Gwamnati Gaba Kan Tsadar Rayuwa
- Malaman addinin musulunci sun yi kira ga masu mulki su saukakawa al’umma halin rayuwa a yau
- Kungiyoyin kiristoci a yankin da Shugaban kasa ya fito sun koka game da tsadar kayan abinci
- Jama’atu Nasrul Islam ta fitar da jawabi cewa ya kamata gwamnati ta duba wahalar da ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Jagororin addinin musulunci da kiristanci a Najeriya, sun yi kira ga hukumomi su samar da abinci ga talakawa.
Wani rahoton Daily Trust ya ce masana addinin sun yi wannan kira a ranar Alhamis, su ka koka cewa jama’a suna shan wahala.
Abinci: Majalisar malamai ta koka
Majalisar malaman musulunci da limamai a Kaduna, tayi kira ga Gwamna Uba Sani ya bada tallafi a duka kananan hukumomi 23.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Aminu Umdah da Sheikh Idris Sabon-Gari sun ce cire tallafin fetur da sauran tsare-tsaren gwamnati sun jawo kuncin rayuwa.
...Kiristoci sun ce rayuwa tayi tsada
Wata kungiyar fastocin darikar Katolika a Najeriya tayi makamancin wannan kira a Ibadan, ta ce an shiga matsin tattalin arziki.
Kungiyar da ta kunshi malaman kiristoci daga Ilorin, Ondo, Oyo, Ekiti da Osogbo sun bayyana matsayarsu a wajen taron addu’o’i.
Kiran Jama’atu Nasril Islam ga Tinubu
Ana haka kuma sai ga The Cable ta kawo rahoto cewa kungiyar nan ta Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta kira taron manema labarai jiya.
Kungiyar JNI da ke karkashin Mai alfarma Sarkin musulmi ta ce akwai hadari ayi watsi da masifar da talakan Najeriya yake ciki a yanzu.
Khalid Aliyu ya fitar da jawabi a matsayinsa na Sakatare Janar, yake cewa ko ta ina jama’a su na kuka da tsadan da kaya suka yi a kasuwa.
Azumi ya zo ga tsadar abinci
Jama’atu Nasril Islam ta ankarar da gwamnati cewa watan azumi ya gabato, ya kamata a dauki mataki kafin lamarin ya kara ta’azzara.
Dr. Khalid ya yi tsokaci game da cafke masu zanga-zanga da aka yi a Kano da Minna tare da jan-kunnen ‘yan kasuwa da ke boye kaya.
Taron kungiyar gwamnoni
Rahoton nan ya zo cewa Gwamnonin jihohi za su kawo dabaru da tsare-tsaren da za su tilasta arahar kayan abinci a kasuwanni.
Mai girma gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya jagoranci zama da aka yi a kan tattalin arziki a matsayin shugaban NGF.
Asali: Legit.ng