Farashin Litar Man Fetur Za Ta Ƙara Yin Tashin Gwauron Zabi a Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana
- Kamfanin mai na ƙasa NNPCL ya musanta rahoton da ke yawo cewa farashin man fetur zai ƙara tashi a Najeriya
- Ya kuma shawarci masu ababen hawa da su kaucewa sayen mai da haɗa cunkoso a gidan mai saboda tsoron ƙara farashi
- Mai magana da yawun NNPC, Olufemi Soneye, ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) Ltd ya musanta raɗe-raɗin cewa za a samu karin farashin litar man Premium Motor Spirit (PMS) wanda aka fi sani da Fetur.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da NNPCL ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu, 2025.
A sanarwan mai ɗauke da sa hannun shugaban sashin hulɗa da jama'a, Olufemi Soneye, NNPCL ya buƙaci masu ababen hawa su kaucewa cunkoson sayen fetur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwan ta kuma ƙara ta tabbatar wa kwastomomi cewa akwai isasshen man fetur maƙare a ma'ajiyar kamfanin mai na ƙasa.
Shin farashin Fetur zai ƙara yin tashin gwauron zabo?
Wani sashin sanarwan ya ce:
"Kamfanin NNPCPL na tabbatar wa ɗaukacin jama’a ƴan Najeriya cewa babu wani kari da za a yi nan gaba a kan farashin litar man motoci (PMS), wanda aka fi sani da fetur.
“NNPCL ya kuma roƙi ‘yan Najeriya da su yi watsi da jita-jita da ba ta da tushe balle makama, ya kuma ba su tabbacin cewa babu wani shiri na sake duba farashin PMS.
“Ana shawartan masu ababen hawa a duk faɗin ƙasar da su guji shiga cunkoson sayen mai cikin yanayin firgici saboda a halin yanzu akwai wadatar Fetur a duk faɗin Najeriya."
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da tsadar rayuwa ke ƙara jefa ƴan Najeriya cikin ƙunci da yunwa sakamakon tashin farashin kayan abinci.
Shin Arewa na goyon bayan Tinubu yanzu?
A wani rahoton na daban Arewacin Najeriya na nan tare da Gwamnatin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu duk da halin tsadar rayuwar da ake ciki.
Ƙungiyoyin kare martabar demokuraɗiyya ne suka bayyana haka a wani taron manema labarai da suka kira a Abuja yau Alhamis.
Asali: Legit.ng