'Yan bindiga sun ga takansu yayin da sojoji suka ceto mata 18 a jihar APC, gwamna ya basu kuɗi

'Yan bindiga sun ga takansu yayin da sojoji suka ceto mata 18 a jihar APC, gwamna ya basu kuɗi

  • Dakarun rundunar sojin Najeriya sun kai samame mafakar ƴan bindiga a Katsina, sun ceto mata 18 da aka yi garkuwa da su
  • Kwamandan rundunar Birgade ta 17 ya ce sojojin sun yi gumurzu da ƴan ta'addan kafin su samu wannan nasara
  • Gwamnatin Katsina karkashin Malam Dikko Raɗɗa ta bai wa kowace mace daga ciki kyautar N100,000 domin su kama sana'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kubutar da wasu mata 18 da aka yi garkuwa da su daga hannun ƴan bindiga a jihar Katsina.

Premium Times ta tattaro cewa sojojin sun mika waɗanda aka ceto din ga gwamnatin jihar karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Radda.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan 'yan ta'adda a jihar Katsina

Dakarun sojin Najeriya sun ceto mata 18 a Katsina
Dakarun Soji Sun Kwato Mata 18 da Aka Yi Garkuwa da Su, Sun Mika Su Ga Gwamnatin Katsina Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Kwamandan Brigade 17 na Rundunar Soji, Oluremi Fadairo, ya ce sojojin sun kai samame maɓoyar ’yan bindigar da ke dazukan Yan-Tumaki da Dan-Ali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa da zuwan dakarun sojin suka fara musayar wuta da ƴan ta'addan wanda daga bisani suka fatattake su tare da ceto matan har su 18.

Mista Fadairo, Birgediya Janar, ya ce daga nan ne sojojin suka mika wadanda suka ceto ga kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Katsina, Nasiru Mu’azu.

Ya kuma jaddada kudirin rundunar sojin Najeriya na ci gaba da yin aiki ba dare ba rana domin maido da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.

Kwamandan ya bukaci jami’an da ke karkashin rundunarsa da su ci gaba da gudanar da irin wannan aikin ceto domin ganin an kubutar da sauran wadanda aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da yawa sun mutu yayin da suka kai farmaki kan jami'an tsaro a jihar Arewa, an kashe sojoji

Gwamna Raɗɗa ya maida hankali kan sha'anin tsaro

Da yake tsokaci kan lamarin, Mu’azu ya jaddada cewa gwamnatin Katsina ta maida hankali kacokan wajen ganin an maido da zaman lafiya na dindindin a jihar.

Mista Mu'azu ya bayyana cewa Gwamna Radɗa ya zuba dukiya mai tsoka a bangaren tsaro, wanda, "har ya fara haifar da sakamako mai kyau."

Bisa haka ya shawarci ƴan bindiga da masu garkuwa da sauran masu aikata miyagun laifuka su tuba tun yanzu ko kuma su fuskanci abinda ba zai musu daɗi ba.

Gwamna ya ba su tallafin N100,000

Daga karshe kwamishinan ya mika naira 100,000 ga kowane daya daga cikin wadanda aka ceto a madadin Gwamna Radda, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, Firdausi Bishir, ‘yar shekara 13 dalibar JSS, ta ce an sace ta ne daga Sayaya kuma ta shafe kwanaki 91 a wurin ‘yan fashin.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN da ministocin Tinubu 2 sun bayyana a gaban majalisa, sun yi bayanai masu muhimmanci

Ta yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba sojojin damar kubutar da su,, kana gode wa gwamna da ya ba su kudi su faraa sana’o’i bayan sun koma gida.

Gwamnan Kaduna ya yi magana kan ƴan bindiga

A wani rahoton kuma Malam Uba Sani ya bayyana hanyoyin da ya kamata a bi domin kawo karshen matsalar tsaro a Arewa maso Yamma.

Gwamnan ya ce tun asuli talauci ne da rashin aikin yi suka kawo matsalar tsaro, don haka bai kamata a bi matakin soji kaɗai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel