Rundunar 'Yan Sanda Ta Bazama Neman Fitaccen Malamin Musulunci Ruwa a Jallo, Bayanai Sun Fito
- Rundunar 'yan sanda a jihar Bauchi ta sanar da neman fitaccen malamin addinin Musulunci ruwa a jallo
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Alhamis 8 ga watan Faburairu a Bauchi
- Sanarwar ta ce ofishin kwamishinan 'yan sanda a jihar na neman Sheikh Idris saboda raina umarnin kotu da ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - Rundunar 'yan sanda a jihar Bauchi ta sanar da neman fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar.
Rundunar ta ayyana neman Dakta Abdul'aziz Idris Dutsen Tanshi ruwa a jallo a yau Alhamis 8 ga watan Faburairu.
Wane umarni rundunar ta bayar?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Alhamis 8 ga watan Faburairu a Bauchi, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce ofishin kwamishinan 'yan sanda a jihar na neman Sheikh Idris saboda raina umarnin kotu da ya yi a baya.
Rundunar ta ce adireshinsa shi ne Dutsen Tanshi kuma ɗan shekaru 63, siriri kuma ya na yawan saka kayan Hausawa.
Mene ake zargin malamin a kai?
Ta kuma bukaci duk wanda ya ke da bayanan da zai sa a kai ga nasarar kama malamin ya tuntubi hukumar.
Idan ba a manta ba, shehin malamin ya na fuskantar shari'a a gaban kotun shari'ar Musulunci da ke Bauchi.
A baya, an ba da belinsa amma ya ki halartar zaman kotun har guda biyu don ci gaba da sauraran karar.
Hakan ya tilasta kotun ba da umarnin cafke malamin saboda kin mata biyayya.
Kotu ta ba da umarnin cafke malamin Musulunci
Kun ji cewa kotun shari'ar Musulunci a jihar Bauchi ta ba da umarnin cafke Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi.
Ana zargin shehin malamin addinin, Sheikh Abdul'aziz da kin mutunta umarnin kotun kan halartar zamanta da aka yi har sau biyu.
Wannan na zuwa ne bayan Shehin malamin ya ki halartar zaman kotun har sau biyu da aka yi a ci gaba da sauraran karar tasa.
Asali: Legit.ng