Nasara Daga Allah: Dakarun Sojoji Sun Samu Gagarumar Nasara Kan 'Yan Ta'adda a Jihar Katsina
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kuɓutar da wasu mata 18 a wani samame da suka kai maɓoyr ƴan ta'adda
- Bayan kuɓutar da mutanen daga hannun ƴan ta'addan, sojojin sun mia su zuwa hannun gwamnatin jihar
- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida wanda ya karɓi mutanen, ya yaba wa sojojin bisa jajircewar da suka nuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - A ranar Laraba dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar kuɓutar da wasu mata 18 da aka yi garkuwa da su tare da miƙa su ga gwamnatin jihar Katsina.
Kwamandan bataliya ta 17 ta sojojin Najeriya, dake Katsina, Birgediya Janar Oluremi Fadairo, ya ce sojojin sun kai wani samame ne a cikin dazukan Yan-Tumaki da Dan-Ali, cewar rahoton Vanguard.
Ya bayyana cewa sojojin sun yi nasarar fatattakar ƴan ta’addan a fafatawar da suka yi, inda suka yi nasarar kuɓutar da mutanen da aka sacen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga nan Fadairo ya miƙa mutanen ga kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Dr Nasiru Mu’azu, rahoton The Guardian ya tabbatar.
Ya kuma jaddada shirin rundunar sojin Najeriya na ci gaba da yin aiki domin maido da zaman lafiya na dindindin a jihar.
Kwamandan ya buƙaci jami’an da ke ƙarƙashin rundunar da su ci gaba da gudanar da irin wannan aikin ceto domin ganin an kuɓutar da sauran waɗanda aka yi garkuwa da su.
Gwamnatin Katsina ta yaba da ceto matan
Da yake mayar da martani, Mu’azu ya jaddada ƙudirin gwamnati na maido da zaman lafiya na dindindin a jihar.
Mu’azu ya bayyana cewa Gwamna Dikko Radda ya zuba jari mai tsoka a ɓangaren tsaro, inda ya ƙara da cewa “kwalliya na biyan kuɗin sabulu".
Kwamishinan ya yabawa sojoji da sauran jami’an tsaro bisa jajircewar da suka yi wajen ganin an dawo da zaman lafiya a jihar, ya kuma buƙace su da su ci gaba da hakan.
Legit Hausa ta tuntuɓi wani mazaunin yankin Yan Tumaki, mai suna Lukman Kabir, wanda ya yaba da wannan nasarar da sojojin suka samu na kuɓutar da mutanen.
Sai dai, ya koka kan yadda har yanzu ƴan bindiga ke cin karensu babu babbaka a ƙaramar hukumar Dan Musa, inda ya ce ƴan bindigan har cikin garin Dan Musa suke shiga suna tafka ta'asa.
Ya yi kiran da a ƙara zage damtse domin ganin an yi maganin ƴan bindigan masu tayar da ƙayar baya a yankin.
Sojoji Sun Halaka Ƴan Ta'adda Masu Yawa a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun halaka ƴan ta'adda masu yawa a wani harin da suka kai a jihar Katsina
Sojojin dai sun yi luguden wuta ne a maɓoyar ƴan ta'addan da ke a Tsaunin Tora cikin ƙaramar hukumar Safana ta jihar.
Asali: Legit.ng