Babban Labari: Sabbin Mambobin Majalisar Wakilai 12 Sun Yi Rantsuwar Kama Aiki

Babban Labari: Sabbin Mambobin Majalisar Wakilai 12 Sun Yi Rantsuwar Kama Aiki

  • Akalla 'yan majalisu 12 ne cikin 15 da hukumar INEC ta ba shaidar cin zabe aka rantsar da su a zauren majalisar tarayya yau Alhamis
  • Daga cikin wadanda suka samu damar halartar taron rantsarwar akwai Sanata Ifeanyi Ubah wanda ya sauya sheka daga YPP zuwa APC
  • Sai dai akwai sauran 'yan majalisar 3 da ba yau za a rantsar da su ba, kuma INEC na ci gaba da gudanar da zabe a wasu jihohi biyu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kakakin majalisar tarayya, Tajudeen Abbas ya rantsar da 12 daga cikin zababbun mambobi 15 da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gabatar a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai kazamin hari jihar Arewa, sun sheke mutum 6 da sace mata 20

Sabbin mambobi 12 sun lashe zaben na ranar Asabar da ta gabata kamar yadda kotu ta ba da umarnin sake gudanar da zabukan domin cike gurbi wasu kujeru a majalisar.

An rantsar da sabbin 'yan majalisun tarayya 12.
An rantsar da sabbin 'yan majalisun tarayya 12. Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Sanata Ifeanyi Ubah wanda kwanan nan ya sauya sheka daga jam’iyyar Young Progressive Party (YPP) zuwa jam’iyyar APC mai mulki ya halarci bikin rantsuwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai har yanzu ba a kammala gudanar da zaben mazabar Jalingo/Yorro/Sing na jihar Taraba da kuma Udenu na jihar Enugu, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Akwai sauran mambobi uku da suka karbi takardar shaidar cin zabe daga INEC da za a rantsar da su nan gaba kadan.

Shugaban majalisar ya gabatarwa da sabbin ‘yan majalisar kwafin dokokin majalisar da kuma ajandar majalisa.

Da wannan sabon ci gaban, yanzu APC na da kusan mambobi 188 da za su ci gaba da zama mafi rinjaye a majalisar.

Kara karanta wannan

Yadda jami’an yan sanda suka yi garkuwa da wani mazaunin Abuja, suka kwashe gaba daya kudin asusunsa

Wadanda suka karbi takardar shedar cin zaben sune: Umar Garba (mazabar Ngaski/Shanta/Yauri, jihar Kebbi -APC); Ifeoluwa Ehindero (AKoko Arewa maso Gabas/Arewa maso Yamma a Ondob - APC).

Sauran sun hada da, Faud Kayode Laguda (mazabar Suru Lere ta a Legos - APC) da Saleh Gabriel Zock (mazabar Kachia/Kangaroo a Kaduna - APC).

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.