Lokaci Ya Yi: Babban Basarake a Najeriya, Joseph Edozien Ya Rigamu Gidan Gaskiya
- Rahotanni da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa Allah ya karbi rayuwar mai martaba Sarkin Asaba, Joseph Chike Edozien
- An ruwaito cewa basaraken ya rasu a yammacin ranar Laraba, sai dai masarautar Asaba bata fitar da rahoto a hukumance ba har zuwa yau
- Sarki Edozien shi ne Asagba na 13 na masarautar Asaba, wanda ya fara shirye-shiryen bukin cikarsa shekara 100 ajali ya cimmasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Basaraken gargajiya na Asaba, babban birnin jihar Delta, Mai martaba Obi (Prof.) Joseph Chike Edozien, ya rasu.
Edozien wanda shi ne Asagba na 13 na Asaba, ya bi sahun kakanninsa zuwa kushewa a ranar Laraba.
Kwanan nan ne Asagba na Asaba ya fara shirye-shiryen bikin cika shekaru 100 a duniya, PM News ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har yanzu masarautar Asaba bata magantu kan mutuwar ba
Mazauna Asaba, babban birnin jihar Delta suka bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga daukacin masarautar Asaba.
Duk da cewa har yanzu fadar ba ta bayyana mutuwar sarkin a hukumance ba, amma wasu majiyoyi da dama sun tabbatar da hakan ga jaridar Niger Delta a Yau.
Har zuwa kammala rubuta wannan rahoton, kokarin samun tabbaci a hukumance daga sakataren fadar, Cif Patrick Ndili, ya ci tura.
Shahararren dan jaridar wasanni a Najeriya ya kwanta dama
A wani labarin makamancin wannan, shahararren dan jaridar nan na wasanni, Kayode Tijani ya rigamu gidan gaskiya.
An ruwaito cewa Kayode ya rasu a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas bayan fama da rashin lafiya.
Yar uwar marigayin, Dokta Ganiyat Tijani ta sanar da mutuwarsa a jiya Laraba, inda ta ce yau Alhamis ne za ayi masa sutura a makabartar Atan da ke Yaba, jihar Legas.
Kadan daga nasarorin da Tijani ya samu a aikinsa
Kafin rasuwar Tijani, ya kasance babban jami'i a kafofin watsa labaran wasanni na SportsXclusive da Sports Focus International kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Haka zalika ya taba rike mukamin babban sakataren watsa labarai na marigayi Chief Alex Akinyele, tsohon ministan wasanni na kasa.
Asali: Legit.ng