Tagwaye masu shekara 200 a duniya
Wasu tagwaye mata da ake tunanin sun fi kowa dadewa a duniya sun cika 100 tare, ma ‘ana su biyu sun yi shekaru 200 ke nan a duniya kuma tare da juna.
‘Yan biyun masu kama da juna, sun kuma yi murnar zagayowar ranar haihuwarsu ne da tare da ‘yan uwa da abokan arziki a wata a ‘yar kwaya-kwaryar liyafa.
Sai dai a maikamakon kyaututtuka, tagwayen sun nemi duk masu kaunarsu da yin sadaka ga masu bayar da agajin gaggauwa na jirgin sama da duk kyautar da ake da shirin ba su da masoya.
Dangane da baiwar da Allagh yayi musu na tsawon rai, tagwayen na cewa, “mun yi bikin murnar shekaru 90 da haihuwa, mun kuma yi murnar shekaru 99 da haihuwa”. Aiki tukuru da kuma cin abinci mai kyau ne sirrinmu na tsawon rayuwa sune za mu iya tunawa.
‘Yan gida daya masu kama daya, Irene da Phylilis sun yi aure tare. Mijin Irene Samuel ya mutu a shekarar 1999 yana mai shekaru 90, mijin Phyllis kuwa Ray Jones, ya mutu yana da shekara 91, a shekarar da wuce.
Sai dai Allah bai ba Irene haihuwa ba, amma Phyllis na da da, daya mai suna Carl, kuma a yanzu shi ya ke kula da tsaffin biyu duk da cewa ba gida guda suke zaune ba.
Ku biyomu a Tuwita a @naijcomhausa
https://youtu.be/JxgqJEGC9zE
Asali: Legit.ng