Babban Jigon APC Ya Yanke Jiki Ya Mutu Yayin da Ya Ke Kallon Wasan Najeriya
- Jigon jam'iyyar APC kuma tsohon dan majalisar wakilai, Cairo Ojougboh, ya yanke jiki ya mutu yayin da yake kallon wasan Najeriya da Arika ta Kudu
- An ce Ojougboh ya fadi ne a lokacin da kasar Afrika ta Kudu ta samu bugun fenariti kan 'yan Super Eagles a wasan kusa da karshe na AFCON 2023
- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi alhinin mutuwar farat daya da dan siyasar na Delta ya yi
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da
Wani jigon jam'iyyar APC kuma tsohon dan majalisar wakjilai, wanda ya wakilci mazabar Ika ta jihar Delta a majalisar tarayya, Cairo Ojougboh, ya mutu.
Ojougboh, wanda ya shahara saboda rashin tsoron fitowa ya yi magana ya kwanta dama ne a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, yayin da yake kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu a gasar AFCON da ke gudana.
Jaridar Leadership ta ruwaito daga majiya mai tushe cewa dan siyasar ya mutu ne a yayin da ake buga wasan fenariti a ragar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce:
"Ya yanke jiki ya fadi a lokacin da aka bayar da fenariti akan Najeriyan yayin gasar AFCON da Kudu ta Afrika a wasan kusa da karshe da aka yi a ranar Laraba a Bouake, Ivory Coast."
Ojougboh, wanda tsohon daraktan ayyuka ne na kwamitin riko na hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC), na daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC da aka kora daga jam’iyyar bisa zargin cin dunduniyar jam’iyyar a zaben 2023.
Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Ika ta Kudu a jihar, Hilary Ibude, ne ya sanya hannu a takardar korar mai kwanan wata 27 ga watan Maris.
Ibude ya bayyana cewa an kori marigayi Ojougboh daga jam'iyyar bayan korafe-korafen da aka shigar a kansa a cikin abin da ya ce yana da nasaba da tsaikon da jam'iyyar ta samu a zaben.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi alhinin rashin a dandalinsa na soshiyal midiya inda ya bayyana marigayin a matsayin abokinsa kuma mai kishin kasa.
Ya rubuta a shafin nasa:
"Mutuwar farat daya da abokina Dr. Cairo Ojougboh ya yi ya sanya ni bakin ciki. Kaunarsa ga kasarmu na da yawa."
Lauya ya zanke jiki ya fadi a kotu
A wani mun ji cewa ajali ya riski wani lauya a ƙofar shiga harabar kotu a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, lauyan ya yanke jiki ya faɗi kuma ya sume nan take, domin bayanai sun nuna ya fita a hayyacinsa a kofar shiga kotu.
Asali: Legit.ng