Yadda Jami’ai Suka Ceto Wasu Mutum 3 Daga Hannun Mai Fataucin Mutane a Jihar Arewa

Yadda Jami’ai Suka Ceto Wasu Mutum 3 Daga Hannun Mai Fataucin Mutane a Jihar Arewa

  • Jami'an Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), sun yi ram da wani mutum a hanyarsa ta fataucin wasu mutane zuwa kasar waje
  • An kuma ceto mutum uku da ake shirin safararsu zuwa Daura inda daga nan za su ketare boda zuwa kasar Nijar kafin su garzaya Libya
  • Iyayen yaran sun tabbatar da cewar da sanensu ake shirin fataucin mutanen saboda talauci da ya yi masu katutu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Jigawa - Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), ta ce ta ceto wasu mutane uku da ake shirin fataucinsu a jihar Jigawa.

Shugaban hukumar NIS a jihar Jigawa, Mista Samson Agada, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka yi a garin Dutse, babban birnin jihar a ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta kirkiri dakarun mutum 7,000 da za su yaki masu tashin farashin Dala

Shugabar hukumar kula da shige da fice ta kasa
Yadda Jami’ai Suka Ceto Wasu Mutum 3 Daga Hannun Mai Fataucin Mutane a Jihar Arewa Hoto: @nigimmigration
Asali: Twitter

Yadda jami'an NIS suka ceto mutanen

Ya ce jami'an hukumar sun kama mutanen ne a ranar Talata da misalin karfe 11:00 na safe, a shingen bincike na Tsamiyar Ilu da ke karamar hukumar Kazaure ta jihar, jaridar Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Agada ya ce mutanen da abin ya ritsa da su, wadanda 'yan asalin jihar Kogi ne sun hada da Ahmed Ibrahim, 25; Ibrahim Rafatu, 17, da Nafisat Jibril, 32.

Ya kuma bayyana cewa an cafke su ne tare da wani da ake zargin mai fataucin mutane ne, Mustapha Zulqarlaini.

Da aka yi masu tambayoyi, mutanen sun tona asiri cewa suna a hanyarsu ta zuwa yankin Daura da ke jihar Katsina ne.

An tattaro cewa daga nan ne za su tsallaka iyakar Najeriya zuwa Jamhuriyyar Nijar, domin su ci gaba da tafiyarsu zuwa kasar Libya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai kazamin hari jihar Arewa, sun sheke mutum 6 da sace mata 20

Sun kuma bayyana cewa suna da wata 'yar uwa da ke zaune a kasar Libya, wacce ita suke shirin zuwa samu a chan.

Shin iyayensu sun san da tafiyar?

Mai fataucin mutanen, Zulqarlaini, ya yi ikirarin cewa shi kawun mutanen ne kuma ya tabbatar da cewar shi ya shirya tafiyarsu daga Kano zuwa Daura.

Shugaban hukumar NIS din ya kuma bayyana cewa da suka tuntubi iyayen yaran, sun ce da sanensu suka kama hanyar tafiyar saboda kangin talauci da suke ciki, rahoton The Cable.

Ya ci gaba da cewa:

"Mutane ne da ake fataucinsu, kuma kan haka za mu mika su ga hukumar NAPTIP."

Ya jaddada jajircewar hukumar na duba masu yin balaguro ba bisa ka'ida ba da kuma masu fataucin mutane akai-akai.

An kama mai fataucin kananan yara

A wani labarin, mun ji a baya cewa rundunar yan sandan Gombe sun yi nasarar damke wasu mutane da ake zargin masu fataucin kananan yara ne a jihar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Mahid Abubakar, ya ce mazauna yankin Barunde ne suka kai wa rundunar kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng