Yan sanda sun gano kungiyar masu safarar yara a Gombe, sun ceto yara 12
Kwamishinan ƴan sanda na jihar Gombe, Shehu Maikudi a ranar Litinin ya gabatar wa manema labarai wasu masu safarar mutane huɗu da ƙananan yara 12.
Maikudi ya ce yan sanda sunyi nasarar kama yan kungiyar ne tare da hadin kai da taimakon iyayen yaran kamar yadda The Punch ta ruwaito.
A cewar Maikudi, wasu daga cikin iyayen sun shigar da rahoto cewa an sace yaransu. An kama daya daga cikin wadanda ake zargin a makon da ta gabata.
DUBA WANNAN: Wata mata mai shekaru 31 ta fada dam ta mutu yayin daukan hotuna
Daga nan ne kuma bincike ya kai rundunar ƴan sandan har zuwa jihar Anambra inda aka kai ƙananan yaran.
"Wacce muke zargin da aka kama ta tsere tun a shekarar 2017; tun lokacin tana ta canja wurin zama, mun gano yara 12 da ke karkashin ta.
"A halin yanzu ba za mu iya cewa dukkan yaran ƴan Gombe bane. Rundunar ƴan sanda da iyayen yara da gwamnatin jihar duk sun taimaka wurin wannan nasarar da aka samu."
Kazalika, wata Hauwa Usman yar asalin jihar Gombe ta ce ta sayar da yara fiye da 20 ga abokan hulɗar ta a Anambra da Asaba.
KU KARANTA: Mutum 4 ƴan gida ɗaya sun mutu a hatsarin mota a Jigawa Read more
Ta ce, na kan sayar da maza a kan kudi N300,000 yayin da mata kuma na kan sayar da su kan kudi N250,000.
A bangaren ta, Nkechi Odiliye wacce ke da gidan marayu a Anambra ta ce ita kuma tana sayar da yaran a kan kudi N750,000.
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Rundunar ƴan sandan jihar Abia a ranar Laraba ta ce jami'anta sun kama wasu mata biyu da ake zargi da fashi da wasu 41 ciki har da mace mai safarar yara.
Rundunar ta ce an kama wadanda ake zargin ne cikin makonni shida da suka gabata.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Janet Agbede ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Ya ce baya da mata uku da aka kama kan zargin fashi da makami, an kama wasu mata ukun da ake zargi da satar yara da wasu maza 40 da ake zargi da wasu laifukan da suka hada da fashi, garkuwa da shiga ƙungiyar asiri.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng