EFCC Ta Tsitsiye Kanin Tsohon Ministan Buhari Kan Badakalar Naira Biliyan 8

EFCC Ta Tsitsiye Kanin Tsohon Ministan Buhari Kan Badakalar Naira Biliyan 8

  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta cafke Abubakar Ahmad Sirika, kanin tsohon ministan sufurin jiragen sama
  • An tattaro cewa, hukumar ta bugi ruwan cikinsa a binciken da ta ke yi na yadda aka karkakatar da biliyoyin kudade daga ma'aikatar sufurin jiragen sama
  • Ana zargin an bai wa Ahmad Sirika, kwangila na biliyan 8 ta kamfaninsa mai suna Engirios Nigeria Limited

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), ta kama Abubakar Ahmad Sirika, kanin tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Abubakar Sirika.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar EFCC ta kama Ahmad Sirika ne a ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairu, kan wani bincike da ake gudanarwa a ma'aikatar sufurin jiragen sama.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai kazamin hari jihar Arewa, sun sheke mutum 6 da sace mata 20

EFCC ta kama kanin Hadi Sirika
EFCC Ta Tsitsiye Kanin Tsohon Minista Sirika Kan Badakalar Naira Biliyan 8 Hoto: FAAN/EFCC
Asali: Facebook

Me yasa EFCC ta tsitsiye kanin Hadi sirika?

An kama kanin tsohon ministan ne, kan wani bincike na badakalar naira biliyan 8 da ake gudanarwa a ma'aikatar karkashin Sirika, lokacin da aka ba shi kwangila duk da cewar shi ma'aikacin gwamnati ne, mataimakin darakta a mataki na 16.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake rike da mukamin minista, ana zargin Sirika da hada baki, cin mutuncin kujerarsa, karkatar da kudaden jama’a, kara farashin kwangila, zamba cikin aminci da kuma karkatar da kudaden da suka kai N8,069,176,864.

A cewar hukumar EFCC, kudaden na kwangilar jiragen sama guda hudu ne daga tsohon ministan zuwa wani kamfani mai suna Engirios Nigeria Limited, mallakin kaninsa, rahoton Leadership.

Hukumar yaki da rashawar ta ce baya ga kasancewarsa shugaban kamfanin, Abubakar shi kadai ne mai sanya hannu kan asusun biyu na kamfanin.

Kara karanta wannan

Kotu ta garkame malamin addini da matarsa saboda babban laifi 1 da suka aikata

EFCC ta tsitsiye shugabannin bankuna

A wani labarin kuma, mun ji cewa hukumar EFCC ta bugi ruwan cikin shugabanni da manyan daraktocin bankunan zamani guda uku.

EFCC ta yi masu 'yan tambayoyi kan badaƙalar kudade sama da naira biliyan 44 da aka gano a ma’aikatar jin kai.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto cewa har ya zuwa ƙarfe 4:55 na yammacin ranar Talata, hukumar na yi wa manyan daraktocin na bankunan Zenith, Providus, da Jaiz tambayoyi a hedikwatarta dake Jabi, Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng