Majalisa Ta Waiwayi Batun Digiri Dan Cotonou, Ta Dauki Muhimmin Mataki

Majalisa Ta Waiwayi Batun Digiri Dan Cotonou, Ta Dauki Muhimmin Mataki

  • Majalisar wakilai za ta bi ɗiddigi kan masu hannu a badaƙalar digirin bogi da aka bankaɗo a ƙasar nan a kwanakin baya
  • Majalisar ta amince za ta yi bincike kan jami'an ma'aikata da hukumomin gwamnatin tarayya masu hannu a badaƙalar bayan gabatar da wani ƙudiri
  • Ƙudirin dai ya buƙace majalisar da ta bincike masu hannu a badaƙalar a tsawon shekara 10 da suka gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta amince da ƙudurin bincikar wasu jami’an ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da ke da hannu a badakalar satifiket ɗin bogi na wasu ɗaliban Najeriya.

Amincewar ta biyo bayan gabatar da wani ƙuduri a zauren majalisar a ranar Laraba, wanda ɗan majalisa mai wakiltar Birniwa/Guri/Kiri-Kasamma na jihar Jigawa, Abubakar Fulata ya gabatar, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta nuna bajinta, ta samu gagarumar nasara

Majalisa za ta yi bincike kan digirin bogi
Majalisa za ta binciki masu hannu a badakalar digirin bogi Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Idan ba a manta ba, a watan Disamban 2023 ne wani ɗan jarida a Najeriya, Umar Audu ya samu digiri a wata jami’a a Cotonou, Jamhuriyar Benin, a cikin makonni shida, sannan kuma ya gudanar da bautar ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani Audu ya zargi jami’an ma’aikatar ilimi da ba a bayyana sunayensu ba a matsayin masu hannu a badaƙalar, wanda hakan ya jawo suka daga masu kishin Najeriya.

Jaridar The Nation ta ce da yake jagorantar muhawara kan ƙudirin, Fulata ya yi kira ga majalisar da ta gano jami’an ma'aikatu da ɗaliban da suka ci gajiyar irin waɗannan cibiyoyi da cibiyoyin karatunsu a cikin shekara goma da suka wuce.

Dalilin yawaitar digirin bogi

Tsohon ministan ilimi, Farfesa Tunde Adeniran, ya ce ƴan Najeriya na zuwa neman digiri na bogi da satifiket a Jamhuriyar Benin da sauran ƙasashe da ke makwabta saboda ƙasar nan na mutunta satifiket ɗin takarda.

Kara karanta wannan

Ana cikin halin matsi a Najeriya, Remi Tinubu ta fadi lokacin da sauki zai zo

Adeniran ya ƙara da cewa cin hanci da rashawa ya kuma taimaka wajen gaggawar samun takardar shaidar digiri na bogi a ƙasashen.

FG Ta Dakatar da Karɓar Digiri Daga Togo da Benin

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ɗauki matakin dakatar da tantancewa da amfani da takardun shaidar kammala digiri daga ƙasashen Jamhuriyar Benin da Togo.

Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne bayan wani rahoto ya yi bayani dalla-dalla kan yadda ake samun kwalin digiri a wata jami’a a Jamhuriyar Benin cikin sati shida kacal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng