Innalillahi: Allah Ya Yi Wa Matar Sarkin Suleja Rasuwa

Innalillahi: Allah Ya Yi Wa Matar Sarkin Suleja Rasuwa

Allah ya yi wa Hajiya Fatima Hussaina Awwal Ibrahim, uwargidan mai martaba sarkin Suleja, Jihar Neja, Mallam Muhammadu Awwal, rasuwa.

An rahoto cewa ta rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a ranar Lahadi kuma an mata jana'iza bisa koyarwar addinin musulunci.

Gwamnan jihar Neja, Muhammadu Umaru Bago, ya mika sakon ta'aziyya ga masarautar Suleja da Sarkin Zazzau Suleja, bisa rasuwar, Daily Trust ta rahoto.

Bago a cikin sakon ta'aziyya da Babban Sakataren Watsa Labaransa, Bolgi Ibrahim, ya fitar ya bayyana rasuwarta a matsayin babban rashi ga masarautar da kuma daukakin jihar.

Ya karfafawa Sarkin Zazzau na Suleja din gwiwa ya dauki rasuwarta a matsayin kaddara daga ubangiji ya kuma dangana, a yayin da ya ke rarrashinsa.

Yayin da ya ke addu'a ga Allah ya gafartawa mammaciyar, gwamnan ya kuma yi addu'a ga Allah ya bai wa iyalanta na kusa da nesa tare da daukakin Masarautar hakurin jure rashinta.

Kara karanta wannan

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya yi wa fitaccen jarumin shirin fim rasuwa

Dakaci karin bayani ...

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel