Kaduna: Jimami Yayin da Fitaccen Farfesa a Najeriya Ya Rasu Ya Na da Shekaru 61 a Duniya
- Allah ya karbi rayuwar fitaccen Farfesa, Yusuf Dankofa a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna
- Marigayin ya rasu da safiyar yau Talata 6 ga watan Faburairu a Kaduna ya na da shekaru 61 a duniya
- Rahoranni sun tabbatar da cewa tuni aka binne marigayin a Kaduna kamar yadda addinin Musulunci ya koyar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - An shiga yanayi bayan rasuwar Farfesa Yusuf Dankofa a yau Talata 6 ga watan Faburairu.
Marigayin ya rasu ne da safiyar yau Talata 6 ga watan Faburairu ya na da shekaru 61 a duniya, cewar TheCable.
Yaushe Farfesan ya rasu a Kaduna?
Rahoranni sun tabbatar da cewa tuni aka binne marigayin a Kaduna kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dankofa ya kasance cikin lauyoyin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a zaben 2019.
Farfesan ya fara aiki ne a tsangayar shari'a a shekarar 1989 a Jami'ar Ahmadu Bello inda daga bisani ya tsallaka zuwa babban lakcara a shekarar 2010.
Ya rike mukamin shugaban tsangayar a Jami'ar daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2014.
Har ila yau, Farfesa Yusuf ya samu daukaka zuwa matsayin Farfesa ne a shekarar 2015.
Martanin Atiku kan rasuwar Farfesan
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi martani kan rasuwar marigayin.
Dan takarar shugaban kasar ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yammacin yau Talata 6 ga watan Faburairu.
Atiku ya ce ya kadu da samun labarin rasuwar Farfesan wanda ya kasance daga cikin lauyoyinsa a zaben 2019.
Dan takarar PDP ya tura sakon jaje ga al'ummar jihar Kano da iyalansa da ma Jami'ar Ahmadu Bello kan wannan rashi.
Fitaccen jarumin fina-finai ya rasu
Kun ji cewa an shiga jimami bayan rasuwar fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Jimi Solanke a jiya Litinin 5 ga watan Faburairu.
Solanke ya rasu ya na da shekaru 81 bayan ya sha fama da doguwar jinya a jihar Ogun.
Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu yayin da aka dauke shi daga kauyensu a karamar hukumar Remo zuwa asibiti.
Asali: Legit.ng