Jihohin arewa 4 da ke sahun gaba a kuncin rayuwa
Sashen kula da cigaban jama'a na majalisar dinkin duniya (UNDP) ya saki sakamakon wani bincike da ya gudanar a kan walwalar jama'a a jihohin Najeriya daga alkaluman da ya tattara a shekarar 2016.
Alkaluman da UNDP ta yi amfani da su kafin fitar da rahoton ta sun hada da; tsawon rai cikin koshin lafiya da sukunin samun ilimin da kuma ingantacciyyar rayuwa.
Jihohin Sokoto, Katsina, Yobe da Bauchi ne a sahun gaba a kuncin rayuwa a fadin Najeriya, kamar yadda rahoton UNDP ya bayyana.
A bangaren jihohin da su ka yiwa ragowar fintinkau a walwala da cigaban jama'a akwai; Abuja, Akwa Ibom, Bayelsa, Ekiti da Legas.
A sahu na biyu a walwalar jama'a akwai jihohin Abiya, Edo, Enugu, Delta, Ribas, Kuros Riba, Imo, Kwara, Kogi, Nasarawa, Ondo da Anambra.
Ragowar su ne Anambra, Ebonyi, Adamawa, Oyo, Taraba, Gombe, Benuwe, Kaduna, Kebbi, Neja, Jigawa da Kano.
Ko a rahoton da UNDP ta saki bayan gudanar da kwatankwacin irin wannan bincike a shekarar 2013, Legas ce a sahun gaba.
DUBA WANNAN: An bankado babbar almundahana a hukumar kula da alhazai ta kasa
Jihar Sokoto da ke mataki na 36 a wancan rahoton na 2013, ta koma mataki na karshe a wannan sabon rahoton. Hakan ya nuna cewar jihar ba ta yi komai ba ta fuskar inganta rayuwa da walwalar jama'ar ta ba.
Jihar Katsina ce ke biyewa Sokoto a mataki na 36, wai a hakan ma ta samu karin daraja ne idan aka kamanta da matsayinta na shekarar 2013.
Sai jihohin Bauchi da Yobe da Maiduguri da Zamfara ke biye da su.
UNDP ta gabatar da wannan sakamakon bincike ne ranar juma'a ta makon jiya a gaban jami'an gwamnatin Najeriya da su ka hada da Ministan kasafi da tsare-tsare, Sanata Udoma Udo Udoma.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com
Asali: Legit.ng