Zargin Satar Kudi: Gwamnatin Kogi Ta Kare Yahaya Bello, Ta Zargi EFCC da Zama Karen Farauta
- Gwamnatin jihar Kogi ta ce akwai 'yan siyasa da ke yunkurin bata sunan tsohon gwamna jihar, Yahaya Bello
- Ta bakin Kingley Fanwo, gwamnatin jihar ta ce zargin da EFCC ke yi na cewar Bello ya saci kudin jihar ba gaskiya ba ne
- Rahotanni sun bayyana cewa hukumar yaki da rashawar tana tuhumar Yahaya Bello da karkatar da naira biliyan 8.2
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kogi - Gwamnatin jihar Kogi ta koka kan yunkurin da wasu ‘yan siyasa ke yi na bata sunan tsohon gwamna jihar, Yahaya Bello.
Ta yi ikirarin cewa 'yan siyasar na amfani da hukumar yaki da yiwa dukiyar ƙasa zagon kasa (EFCC) wajen tozarta tsohon gwamnan.
Gwamnatin jihar ta kuma ce EFCC ta sake kitsa wani tuggun na cewa Bello ya karkatar da kudin jihar a watan Satumbar 2023, watanni hudu kafin hawa kujerar gwamnan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC ta zama karen mafarautar 'yan siyasa - Fanwo
Kwamishinan watsa labarai na jihar Kogi, Kingley Fanwo a cikin wata sanarwa ya ce EFCC na cike da gurbatattun mutane da ke rusa manufar Shugaba Tinubu na yaki da rashawa.
Ya ce:
"Mun ga cewa ana tuhumar Yahaya Bello da karkatar da sama da naira biliyan 8.2 a watan Satumbar 2015 a Abuja.
"Wannan ya nuna cewa hukumar EFCC ta zama karen mafarauta wacce ke gaggawar gogawa Yahaya Bello kashin kaji, amma ta yi kitso ne da kwarkwata."
Gwamnatin Kogi ta ce babu kudin da aka sata a jihar
Kwamishinan ya ce tuhumar da hukumar ke yi abar dariya ce, domin Yahaya Bello ya shiga ofis ne a ranar 27 ga watan Janairu, The Guardian ta ruwaito.
A cewar sa babu yadda za a yi ace Bello ya hada kai da wani Abdulaalami Hudu, kashiya na gwamnatin Kogi wajen karkatar da kudin a watan Satumba tunda bai hau mulki ba.
Ya ci gaba da cewa:
"Yahaya Bello ba shi da wata alaƙar kudi da gwamnatin jihar Kogi gabanin zama gwamna, don haka makirci ne kawai hukumar da wasu 'yan siyasa ke kullawa."
Gwamnatin jihar sai kuma ta gargadi 'yan koren siyasa da su guji tsoma baki a harkokin jihar tana mai jaddada cewa babu wasu kudi na jihar da aka gano sun bata.
Kogi: Yan bindiga sun tare motoci biyu, sun sace fasinjoji
A wani labarin daga jihar Kogi, wasu 'yan bindiga sun tare wasu manyan motocin alfarma guda biyu a hanyar su ta zuwa Abuja inda suka sace fasinjojin ciki.
Wani daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da matarsa, ya bayyana cewa masu garkuwan sun kira shi a waya inda suka nemi naira miliyan 15 kudin fansa.
Asali: Legit.ng