Rudani Yayin da Dan Takarar Gwamna a PDP Ya Gurfana a Gaban Kotu Kan Zarge-zarge, an Fadi Dalilai
- Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Ogun, Ladi Adebutu ya gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya
- An zargin Adebutu kan laifukan guda bakwai da suka hada da badakalar makudan kudade da sauran laifuka
- Lauyan wadanda ake karar, Gordy Uche ya roki kotun ta bar wadanda ake zargin don ci gaba da morar belin da aka ba su tun farko
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ogun - An gurfanar da dan takarar gwamnan jihar Ogun a jamiyyar PDP, Ladi Adebutu a Babbar Kotun Tarayya.
An zargin Adebutu kan laifuka guda bakwai da suka hada da badakalar makudan kudade da sauran laifuka.
Mene ake Adebutu da aikatawa?
Yayin zaman kotun a yau Talata 6 ga watan Faburairu an gurfanar da takarar jami'yyar PDP da wasu mutane bakwai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan rashin nasara da Ladi Adebutu ya yi a Kotun Koli, TheCable ta tattaro.
Shugaban jam'iyyar APC a jihar a Ogun, Yemi Sunusi a shekarar 2023 ya maka Adebutu kan zargin siyan kuri'u a zaben watan Maris.
Dukkan wadanda ake zargin da aikata laifukan su bakwai sun musanta hannu a cikin zarge-zarge.
Lauyan wadanda ake karar, Gordy Uche ya roki kotun ta bar wadanda ake zargin don ci gaba da morar belin da aka ba su tun farko.
Martanin lauyoyi kan zarge-zargen
Yayin da Uche ya roki ta bai wa Adebutu beli tun da shi ya kawo kansa kotun da karan kansa, cewar The Guardian.
Sai dai bukatar lauyan ta samu tasgaro bayan lauyan masu gabatar da kara Rotimi Jacobs ya kalubalanci bukatar.
Bayan sauraran dukkan bangarorin, Mai Shari'a, Abiodun Akinyemi ya ba da belin Adebutu kan kudi naira miliyan daya.
Daga bisani ya dage ci gaba da sauraran karar har zuwa ranar 7 ga watan Faburairu na wannan shekara.
EFCC ta kama kanin Ministan Buhari
Kun ji cewa Hukumar EFCC ta yi nasarar cafke kanin tsohon Ministan harkokin jiragen sama.
Ana zargin Abubakar Ahmed Sirika da zargin badakalar biliyan 8 yayin da hukumar ta yi nasarar kwato biliyan wuta.
Asali: Legit.ng