Tinubu Ya Fito Karara Ya Fadawa Atiku Yadda Ya Samu Najeriya Daga Hannun Buhari
- A wajen yi wa Atiku Abubakar martani, Bola Tinubu ya fadi halin da ya tsinci gwamnatin Najeriya
- Shugaban kasar ya ce an dauki shekara da shekaru tattalin arziki yana zazzabi kafin ya dare mulki
- Alhaji Atiku ya soki yadda gwamnatin Bola Tinubu ta ke neman shawo kan matsalolin Najeriya
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi ikirarin ya karbi mulkin kasar nan ne a mummunan yanayi na tattalin arziki.
Wannan bayani ya na cikin martanin da shugaban Najeriyan ya aikawa Atiku Abubakar wanda ya soki rikon da yake yi.
Raddin ya fito ne ta ofishin Bayo Onanuga wanda yake taimakawa shugaban kasar a wajen harkokin yada labarai da dabaru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya caccaki Atiku
Bayo Onanuga yake cewa Atiku Abubakar da yake kukan gwamnatin Tinubu ta kawo kuncin rayuwa, bai kawo wata mafita ba.
A lokacin da ya tsaya takara, hadimin shugaban kasar ya ce Atiku bai kawo wasu shawarwari dabam da za su taimaka ba.
Gwamnatin Tinubu ta kuma ce duka manyan ‘yan takara a zaben 2023 sun yarda akwai bukatar a janye tsarin tallafin fetur.
Jawabin Onanuga ya ce Tinubu ya bambanta da Wazirin Adamawa ne kurum a batun saida NNPC da sauran kadarorin kasa.
Shugaba Tinubu yana sa rai a karshe za a ji dadin manufofin tattalin arzikin da ya kawo kamar daidaita farashin kudin ketare.
Martanin Tinubu ga Atiku Abubakar
"Atiku ya fito fili ya fadi gaskiya cewa shugaba Tinubu ya gaji tattalin arziki mai rauni, wanda dole yana bukatar garambawul."
"An shafe shekaru da yawa da matsalar kudi, karancin kudin shiga, da tulin bashin gida da waje da nauyin biyan bashi mai yawa."
"Kasafin kudin kasar 2023 da Tinubu ya iske ya nuna 97% na kudin da aka samu zai tafi ne a biyan bashi, babu kudin kirki na ayyuka."
- Bayo Onanguga
Hadimin yake cewa saboda a ceto tattalin arziki ne gwamnatinsu ta dauki matakan da a yau irinsu ‘dan takaran PDP suna sukarsa.
Gwamna Abba zai hadu da Tinubu
An ji Gwamnan Kano yana neman yadda farashin kaya da abinci za su sauko kafin watan azumi don haka zai gana da Bola Tinubu.
Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf zai yi rabon abinci a kananan hukumomin Kano domin ya rage radadin yunwa da ake ciki.
Asali: Legit.ng