Yan Bindiga Sun Mutu Yayin da Suka Kai Farmaki Kan Jami'an Tsaro a Jihar Arewa, An Kashe Sojoji
- Ƴan bindiga sun kai hari sansanin sojoji da ke makarantar sakandiren gwamnati a Dauran, karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara
- Rahoto ya nuna maharan sun kai harin ɗaukar fansa ne amma sojoji sun kashe su da yawa a musayar wuta ranar Litinin
- Mazauna garin sun bayyana cewa sojoji biyu da ɗan sanda ɗaya sun mutu a harin, amma sun kashe ƴan bindiga da yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Yan bindiga masu yawa, sojoji biyu da ɗan sanda ɗaya sun rasa rayukansu a wani kazamin gumurzu da aka yi ranar Litinin a jihar Zamfara.
Lamarin ya auku ne lokacin da ƴan bindigar suka kai farmaki kan jami'an tsaro da ke makarantar Sakandaren Gwamnati, Dauran a karamar hukumar Zurmi.
Wasu majiyoyi da dama daga garuruwan Dauran da Zurmi sun shaida wa Premium Times cewa ‘yan ta’addan sun kaddamar da harin ne da misalin karfe 9:30 na safe domin daukar fansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asalin abinda ya jawo harin
A cewarsu, maharan sun kai harin ɗaukar fansa ne bayan sojoji sun damke ɗaya daga cikinsu wanda mazauna yankin suka tona masa asiri ranar Lahadi.
Wani shugaban al'umma da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:
"Wasu mazauna garin da aka taba yin garkuwa da su ne suka gano ɗan bindiga a kasuwar ranar Lahadi, nan da nan suka sanar da sojojin da ke zaune a garin.
"Ba tare da ɓata lokaci ba dakarun sojojin suka cafke wanda ake zargin suka yi awon gaba da shi, wannan abun da ya faru shi ne ya jawo harin."
An ce tawagar ƴan bindiga biyu ne suka kutsa kai cikin makarantar sakandiren wadda yanzu ta koma sansanin sojoji.
Adadin rayukan da aka rasa a gumurzun
Abubakar, wani shugaban matasa a Zurmi ya kara da cewa:
"Mafi yawancin sojojin na cikin azuzuwa, waɗanda suka zama ɗakunansu na kwana kwatsam suka fara jin ƙarar harbe-harbe. Sojoji biyu da ɗan sandan da aka kashe suna kan aiki ne a ƙofar shiga.
"Sun yi kokarin maida martani da farko kafin sauran sojojin su kawo musu ɗauki."
Ya kara da cewa dakarun sojin sun kashe ƴan bindiga masu yawa amma gawarwakin biyu kaɗai aka gani saboda ƴan ta'addan sun kwashe sauran sun gudu.
Kakakin Operation Hadarin Daji, Ibrahim Yahaya da jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Zamfara, Yazid Abubakar, ba su ɗaga kiran da aka musu kan harin ba.
Wani mazaunin ƙaramar hukumar, Nafi'u Zurmi, ya shaida wa Legit Hausa cewa tabbas lamarin ya auku kuma dakarun soji sun cancanci a yaba musu sosai.
Ya kuma da ƙara addu'ar Allah ya ci gaba da taimakawa jami'an tsaro a yaƙin da suke da waɗannan miyagun.
Mutumin ya ce:
"Haka zancen yake, an yi musayar wuta mai tada hankali tsakanin jami'an soji da ƴan bindiga a garin Dauran, mai nisan kilomita 7 tsakaninsa da cikin garin Zurmi.
"Muna fatan Allah ya ƙara bai wa jami'an tsaron mu nasara a kan waɗannan mara sa tausayin."
Uba Sani ya gano hanyar kawar da ƴan bindiga
A wani rahoton kuma Malam Uba Sani ya bayyana hanyoyin da ya kamata a bi domin kawo karshen matsalar tsaro a Arewa maso Yamma.
Gwamnan ya ce tun asuli talauci ne da rashin aikin yi suka kawo matsalar tsaro, don haka bai kamata a bi matakin soji kaɗai ba.
Asali: Legit.ng