'Yan Sanda Sun Cafke Rikakken Dan Bindiga a Kano, Bayanai Sun Fito

'Yan Sanda Sun Cafke Rikakken Dan Bindiga a Kano, Bayanai Sun Fito

  • Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanar da cafke wani riƙaƙƙen ɗan bindiga a ƙaramar hukumar Karaye ta jihar
  • Jami'an rundunar sun cafke ɗan bundigan ne wanda ya tsero daga dajin Birnin Gwari saboda rikicin cikin gida da suke yi a sansaninsu
  • Kwamishinan ƴan sandan Kano ya bayar da umurnin tura ƙarin jami'ai domin kare iyakokin jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wani ɗan bindiga mai suna Isah Lawal mai shekara 33, wanda ya fito daga yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Jaridar Leadership ta ce Lawal wanda ya ƙware a harkar fashi da makami, garkuwa da mutane, da satar shanu, an kama shi ne a wani samame da jami’an ƴan sanda ƙarƙashin jagorancin SP Aliyu Mohammed Auwal suka gudanar a jihar Kano.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kan jami'an tsaro a Arewa, sun halaka mutum 4

'Yan sanda sun cafke dan bindiga a Kano
'Yan sandan Kano sun yi caraf da dan bindigan da ya tsero daga Kaduna Hoto: Kano State Police Command
Asali: Twitter

A ranar 4 ga watan Janairun shekarar 2024 ne aka kai samamen a ƙaramar hukumar Karaye ta jihar da ke kan iyakar Kaduna da Kano, inda aka kwato shanu 55 da tumakai shida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanda ake zargin, mazaunin ƙauyen Kaya da ke ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, ya amsa cewa ya gudu daga sansaninsu na ƴan bindiga a Maidaro da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari sakamakon rikicin cikin gida da suke yi.

Meyasa ɗan bindigan ya dawo Kano?

Bayanin da Lawal ya yi a lokacin binciken ya nuna cewa ya koma jihar Kano, musamman dajin Gwarzo-Karaye, sakamakon mutuwar ɗaya daga cikin shugabanninsu, Bashir na Malumfashi, a yayin arangama da wata kungiyar ƴan bindiga da suke gaba da juna.

Mataimakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano, ASP Abdullahi Hussaini, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, ya tabbatar da kama ɗan bindigan, rahoton PM News ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da 'mata 55' ƴan rakon amarya ɗaki a jihar Arewa

ASP Abdullahi ya yaba da ƙoƙarin jami’an ƴan sandan, ya kuma bayyana cewa kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ya umurci tura ƙarin jami'ai da kayan aiki don kare dukkan iyakokin jihar Kano.

Ƴan Sanda Sun Kai Samame Maɓoyar Ƴan Bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an ƴan sanda ƴaƙi da masu garkuwa da mutane sun cafke mutum shida da ake zargin masu garkuwa ne a birnin tarayya Abuja.

Ƴan sanda sun kama masu garkuwan, da suka kunshi maza huɗu da mata biyu yayin da suka kai wani samane sansaninsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng