An Shiga Jimami Bayan Aukuwar Wani Mummunan Hatsarin Mota da Ya Salwantar da Ran Mutum 6
- An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a jihar Ebonyi wanda ya salwantar da ran mutum 11
- Hatsarin motan wanda ya ritsa da motoci masu yawa ya kuma jawo wasu mutum 11 sun samu munanan raunuka
- Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar ta tabbatar da aukuwar harin wanda ta ce ya ritsa da mutum 17
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ebonyi - Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) ta tabbatar da cewa mutum shida sun mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kwanar Onueke a hanyar Afikpo zuwa Abakaliki a jihar Ebonyi.
Kwamandan hukumar FRSC a jihar, Igwe Nnabuife ya shaida wa manema labarai cewa hatsarin ya rutsa da mutum 17, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Nnabuife ya kuma bayyana cewa mutum shida sun mutu, yayin da mutum 11 suka samu munanan raunuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Nnabuife, hatsarin ya haɗa da motoci uku da manyan motoci guda biyu da wata motar bas ta kasuwanci mallakar Peace Mass Transit, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Yadda mummunan hatsarin motan ya auku
A kalamansa:
"Ya faru ne da misalin ƙarfe 11:50 na safiyar ranar Lahadi a Onuwedu, kwanar Onueke, ƙaramar hukumar Ezza ta Kudu a Ebonyi.
"Hatsarin ya ritsa da motoci da yawa inda ya auku sakamakon wucewar ganganci.
"An kai waɗanda suka mutu zuwa ɗakin ajiyar gawarwaki da ke asibitin koyarwa na tarayya na Alex Ekwueme da ke Abakaliki, yayin da waɗanda suka jikkata ke samun kulawa.
"Muna shawartar direbobi da su kasance masu haƙuri yayin tuƙi. Kodayaushe su yi biyayya ga dokokin hanya da ƙa'idodin tuƙi. A guji tuƙi mai haɗari da wuce gona da iri don ceton rayuka."
Amarya Ta Rasu a Hatsarin Mota
A wani labarin kuma, kun ji wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Neja ya salwantar da ran wata amarya da ƙawayenta.
Hatsarin motan dai ya auku ne a lokacin da ake tafiya da amaryar domin kai ta ɗakin mijinta bayan kammala bikin aurensu.
Asali: Legit.ng