An Gagara Gano Inda Aka Kai Bashin da Gwamnatin Buhari Ta Karbo, 'Dole a Bincika'
- SERAP ta na so gwamnatin Bola Tinubu ta binciko gaskiyar inda aka kai bashin da IMF ta bada
- Kolawole Oluwadare ya dogara da bayanan da aka samu daga rahoton mai binciken kudi na kasa
- Kungiyar tana so a dauki mataki muddin ta tabbata an karkatar da dukiyar da aka aro daga waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - SERAP mai kokarin ganin an bi diddiki, tayi kira na musamman ga Bola Ahmed Tinubu ya binciki wasu bashi da aka karbo.
Punch ta ce kungiyar SERAP tana so ayi bincike a kan inda aka kai $3.4bn da gwamnatin tarayya ta karbo aro wajen hukumar IMF.
Hakan ya zama dole ne bayan da aka ji cewa babu wasu takardun da ke nuna inda aka kai wannan bashi da aka ci a shekarar 2020.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoto zai jefa gwamnatin Buhari a matsala
Rahoton da aka samu daga babban mai binciken kudi na gwamnatin tarayya, ya fallasa abubuwan da suka faru a gwamnatin baya.
Tun da babban mai binciken kudi ya fitar da wannan rahoto, Kolawole Oluwadare ya aika wasika cewa akwai bukatar a gano gaskiya.
Kolawole Oluwadare shi ne mataimakin kungiyar ta SERAP da ta matsawa gwamnati.
Buhari: SERAP za ta je kotu a kan bashin IMF
Wasikar da Oluwadare ya sa hannu ta fito ne a ranar Asabar, ta ce ko dai a hukunta wadanda suka ci amana, ko a kai kara a kotu.
Idan har akwai hujjojin da ke tabbatar da kudin da aka karbo aro sun yi kafa, SERAP ta ce dole a dawo da su cikin baitul-malin kasar.
Kungiyar ta ce al’umma na neman ganin an yi abubuwa da gaskiya, kuma wajibi ne ayi maganin masu barna da dukiyar Najeriya.
Sahara Reporters ta ce SERAP tana so a dauki matakin da ya dace mako guda da fitowar budaddiyar wasikar da Oluwadare ya rubuta.
IMF: Takardar shugaban kungiyar SERAP
"Idan ba mu ji komai daga gare ku zuwa lokacin ba, SERAP za tayi tunanin daukar matakin shari’a domin tursasawa gwamnatinku tayi abin da jama’a suke bukata."
"Zargin rashin gaskiya wajen batar da bashin IMF kamar yadda Baban mai binciken kudi ya gabatar ya nuna kawo tasgaro wajen cigaban tattalin arzikin kasar."
- Kolawole Oluwadare
Buhari ya jawowa Gwamnoni aiki
Gwamnoni kimanin 150 da manyan Ministocin Abuja 8 aka yi daga 1999 zuwa bana, an ji labari SERAP na barazanar maka su duka a kotu.
SERAP tana zargin Gwamnonin suna lakume abin da aka warewa kananan hukumominsu, an nemi ayi bayanin inda aka kai N40tr.
Asali: Legit.ng