Hukumar FCTA Za Ta Kori ’Yan Kasuwar Gwarinpa Daga Shagunansu? Gaskiyar Magana Ta Bayyana

Hukumar FCTA Za Ta Kori ’Yan Kasuwar Gwarinpa Daga Shagunansu? Gaskiyar Magana Ta Bayyana

  • An ba 'yan kasuwa da ke zama a kan titin N16, Gwarinpa wa'adin kwanaki biyar su kwashe kayan su daga kan titin
  • Hukumar gudanarwar babban birnin tarayya (FCTA) ce ta ba su umurnin ta bakin Mukhtar Galadima
  • Rahotanni sun bayyana cewa tun a watan Disambar 2023 ne aka nemi su tashi don gudanar da aikin fadada titin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar gudanarwar babban birnin tarayya Abuja (FCTA) ta ba 'yan kasuwa da ke kan titin N16 a Gwarinpa wa'adin kwashe 'yan komatsansu.

Sashen sa ido kan bunkasa FCT na hukumar ya bayar da sanarwar, inda ya nemi 'yan kasuwar su kwashe kayan su nan da ranar Alhamis mai zuwa.

Kara karanta wannan

Ina sukar biyan da kudin fansa a baya, sai da aka sace ni na gane, tsohon shugaban DSS ya magantu

Wike zai tashi 'yan kasuwa a Gwarinpa
Wata sabuwa: Wike ya ba 'yan kasuwa a Gwarinpa wa'adin kwana 5 su kwashe kayansu. Hoto: @GovWike
Asali: Facebook

Tun a watan Disamba aka so tashin 'yan kasuwar

Daraktan sashen, Mukhtar Galadima, ya ba da umurnin a wani taron masu ruwa da tsaki da ya hada da shugabannin kungiyar 'yan kasuwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tun a watan Disamba aka ba da aikin fadada titin, amma 'yan kasuwar suka bijirewa kiraye-kirayen 'yan kwangilar na su tashi, Nigerian Tribune ta ruwaito.

A cewarsa, wa'adin da aka debarwa aikin na ta tafiya ba tare da 'yan kwangilar sun iya yin komai ba saboda taurin kan 'yan kasuwar.

Za a samar wa 'yan kasuwar matsugunni na daban

Ya ce idan har ba a aiwatar da aikin akan lokaci ba, to kudin da aka ware don aiki zai ci gaba da hauhawa wanda ya sabawa tsarin wannan gwamnati.

Dangane da roko daga shugaban masu karbar haraji na Abuja akan samar da wata kasuwar, Vanguard ta ruwaito daraktan ya ce akwai yiyuwar samar da matsugunni ga 'yan kasuwar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta dauki gagarumin mataki bayan 'yan bindiga sun kwashe 'yan kai amarya 60

An ci tarar kamfanin Amurka kan tauye hakkin ma'aikaci Musulmi

A wani labarin kuma, wata kotu a Amurka ta ci tarar kamfanin Blackwell tarar dala 70,000 kan tilasta wani ma'aikaci Musulmi aske gemunsa a lokacin da zai soma aiki da kamfanin.

Rahotanni ssun bayyana cewa kamfanin ya ba mutumin zabi akan aikinsa ko addininsa, wanda kotun ta ce ya saba da dokar daidaito ta daukar aiki a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.