‘Yan kwangilar China sun sa lokacin da za a gama aikin jirgin kasan da zai hada Kano da Kaduna

‘Yan kwangilar China sun sa lokacin da za a gama aikin jirgin kasan da zai hada Kano da Kaduna

  • China Civil Engineering Construction Corporation suna aikin dogo a Najeriya
  • Kamfanin sun ce za a gama titin jirgin kasan Kano zuwa Kaduna a watanni 18
  • Akwai yiwuwar a karkare wannan aiki kafin Muhammadu Buhari ya bar ofis

Shugabannin kamfanin kwangilar China Civil Engineering Construction Corporation na kasar Sin, sun yi imaganar aikin dogon Kano zuwa Kaduna.

Yaushe CCECC za su gama aiki?

Jaridar The Guardian ta rahoto kamfanin na China Civil Engineering Construction Corporation yana cewa za a gama kwangilar ne a cikin watanni 18.

Wani babban ma’aikacin kamfanin CCECC ya shaida wa manema labarai haka a wurin da ake aikin a Zawachiki, a karamar hukumar Dawakin Tofa.

Da yake magana da ‘yan jaridar a makon nan, Muhammad Kabir ya yi alkawarin cewa za a karkare aikin tun kafin lokacin da aka sa ran za a gama.

Kara karanta wannan

Ana zargin Shugaban Majalisa da karbar cin hancin Naira Biliyan 4 domin ya canza zubin PIB

Muhammad Kabir wanda shi ine jami’in da ke lura da ma’aikatan CCECC yace tuni an baza ma’aikata zuwa wuraren da za ayi aikin titin jirgin kasan.

Aikin jirgin kasa
Titin jirgin kasa a Najeriya Hoto: von.gov.ng
Asali: UGC

Ma'aikata sun yi damara

Dazu jaridar ta rahoto Kabir ya na cewa leburori sun fara shirin aikin tun bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin a watan Yuli.

A cewarsa, an dauko ma’aikata daga Ibadan domin su zo suyi wannan aiki a yankin Arewacin kasar.

“Tuni mun tattaro ma’aikatanmu daga garin Ibadan zuwa jihohin Kano da Kaduna domin ganin an yi maza an kammala wannan kwangilar.”

Idan an bi lissafin China Civil Engineering Construction Corporation, akwai yiwuwar a kaddamar da wannan titin jirgi a farkon watannin shekarar 2023.

Za a kashe zunzurutun kudii fam Dala biliyan 1.2 wajen yin wannan titin dogo mai tsawon kilomita 203.

Kara karanta wannan

Yadda aka jefa ni kurkuku na shekara 1 a lokacin Abacha - Sanusi ya bude faifan da ba a tabawa

Titin jirgin Kano - Kaduna

A lokacin da aka kaddamar da shirin wannan aiki, shugaban kasa yace zai taimaka wajen zirga-zirga daga Kano zuwa Kaduna har birnin tarayya, Abuja.

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta na son ganin manyan birane sun hadu ta jirgin kasa. Akwai maganar jan hanyar jirgi har zuwa Maradi a kasar Nijar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel