An Shiga Tashin Hankali Bayan Mahara Sun Sace Manya Kuma Fitattun Malaman Addini 2 a Jihar Arewa
- An shiga tashin hankali bayan mahara sun sace manya kuma fitattun malaman addinin Kirista a jihar Plateau
- ‘Yan bindigan sun yi awun gaba da Fasto Kenneth Kanwa da kuma Fasto Jude Nwachukwu a karshen makon nan
- Faston cocin St. John Mary Vianney, Cornelius Nweke ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Lahadi 4 ga watan Faburairu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau – ‘Yan bindiga sun yi awun gaba da fitattun Fastoci a cocin Kwande da ke Shendam a jihar Plateau.
Lamarin ya faru ne a karhsen mako da ya wuce inda maharan suka sace Fasto Kenneth Kanwa da Jude Nwachukwu.
Yaushe aka sace Fastocin 2 a jihar Plateau?
Rahotanni sun tabbatar da cewa maharani sun dauke malaman addinin zuwa wani wuri da ba a sani ba, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban Faston cocin St. John Mary Vianney, Cornelius Nweke ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Lahadi 4 ga watan Faburairu.
Fasto Cornelius ya roki dukkan coci-coci da su taya su da addu’a don samun nasarar kubutarsu.
Sace malaman addinin ya jefa tsoro a zukatan mazauna yankin inda Fasto Nweke ya bukaci a kwantar da hankula.
Wane martani rundunar 'yan sanda ta yi?
Faston ya kuma bukaci mutane su guji yada jita-jita inda ya bukace su da su yi addu’a don neman kubutarsu, kamar yadda Newstral ta tattaro.
Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, DSP Alfred Alabo bai samu damar yin martani ba saboda rashin samun wayarsa.
Jihar Plateau na shan fama da hare-haren ‘yan bindiga da kuma yin garkuwa da mutane a kusan kullum a jihar.
Fasto ya tona asirin masu juya Tinubu
Kun ji cewa Fasto Olabisi Adegboye ya bayyana yadda wadansu mutane ke juya gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a Najeriya.
Fasto Olabisi ya ce tabbas mutanen sun kasance masu son rai sosai inda ya ce su ke hana shi yin abin kirki.
Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin mawuyacin hali a kasar tun bayan cire tallafin mai da shugaban ya yi.
Asali: Legit.ng