An Rasa Lantarki a Jihohin Arewa 4 Yayin da Tashar Wuta Ta Samu Muguwar Tangarda

An Rasa Lantarki a Jihohin Arewa 4 Yayin da Tashar Wuta Ta Samu Muguwar Tangarda

  • Legit Hausa ta samu labari an samu daukewar wuta a garuruwa da yawa a safiyar ranar Lahadin nan
  • Kaduna Electric ta fitar da sanarwa cewa wutar lantarki ta janye masu don haka aka shiga cikin duhu
  • Ana sa ran da zarar abubuwa sun dawo daidai, wuta za ta dawo a duka wuraren da abin ya shafa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Jihohi akalla hudu ba su da wutan lantarki a daidai lokacin da mu ke tattara rahoton nan a ranar Lahadi.

Jihohin Najeriyan da abin ya shafa kamar yadda muka fahimta su ne: Kaduna, Sokoto, Zamfara, sai kuma jihar Kebbi.

Lantarki
Wutar lantarki ta dauke a yau Hoto: Heritage Times, The Glitters
Asali: UGC

Kaduna Electric sun rasa lantarki

Abin da ya faru shi ne kamfanin lantarkin da ke aiki a jihohin nan sun rasa kaso mafi tsokan wutar da ake aiko masu.

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Kano, Jigawa Ba Su Fama Da Matsalar 'Yan Bindiga: Shehu Sani Ya Magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban sashen sadarwa na kamfanin Kaduna Electric, Abdulazeez Abdullahi ya tabbatar da wannan a yau Lahadi.

Malam Abdulazeez Abdullahi ya ce da zarar wuta ta dawo hannunsu, al’umma za su fita daga halin da suka shiga ciki.

Kamfanin ne yake da alhakin raba wuta a wadannan jihohin Arewa maso yamma.

Jawabin kamfanin lantarki

"Shugabannin Kaduna Electric suna sanar da masu hulda da su cewa sun rasa wuta saboda haka ake fama da rashin wuta a Kaduna, Sokoto, Zamfara da Kebbi."
"Za a saki wuta ga masu hulda da mu da zarar mun samu lantarki a cibiyoyin da ke yankunan mu."

- Kaduna Electric

Babu wutar lantarki a Najeriya?

Kaduna Electric ta fitar da sanarwar nan a shafin Facebook.The Guardian dai ta ce abin ya shafi daukacin kasar ne.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya yi magana mai zafi bayan fashewar wani abu ta yi ajalin rayukan bayin Allah

Rahoton da aka samu ya ce daga 2, 47 MW sai da ta kai 31MW suka rage da na’urorin suka dauke da karfe 11:51 na safiya.

Wasu mazaunan garin Zariya sun tabbatarwa Legit da cewa an shafe awanni ba su ga hasken wuta ba a duk yau ba.

Da muka tuntubi wasu da ke Kaduna, sun ce tun kimanin karfe 11:00 aka dauke wutan, an yi awanni ba a gan ta ba.

Punch ta ce kamfanonin raba wutar lantarki masu niyyar yin karin kudi ba su yi cikakken bayanin abin da ya faru ba.

Matsalar lantarki a Najeriya

Hakan ya faru ne kwanaki kadan bayan Ministan lantarki yayi hobbasa domin ganin an magance irin wannan matsala.

Bayo Adelabu ya zauna da kamfanonin da ke samarwa da raba wuta, ya koka kan yadda ake fama da karancin lantarki.

Ministan ya ce abin ya tabarbare bayan an yi bikin kirismeti da sabuwar shekara da wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng