Yobe: Mayakan Boko Haram Sun Kai Hari a Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe, Sun Kashe Mutum 2
- Rahotanni a safiyar Lahadi na nuni da cewa Boko Haram ta kai farmaki wata cibiyar tattara sakamakon zabe da ke jihar Yobe
- A yayin harin, an ruwaito cewa sun kashe mutane biyu nan take, daga bisani kuma jami'an tsaro sauka fatattake su
- Hukumar zabe ta kasa (INEC) na tsaka da tattarawa tare da sanar da sakamakon zaben cike gurbin majalisar Yobe ta Gabas aka kai harin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Yobe - Mayakan Boko Haram sun kashe mutum biyu a a wata cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Kuareta, kilo mita 20 nesa da garin Damaturu.
Gwamnatin jihar Yobe ta tabbatar da kai wannan farmaki a garin da ke kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri, kamar yadda shafin talabijin na AIT ya ruwaito.
A cewa hadimin gwamnan jihar kan tsaro, Manjo Janar Dahiru Abdulsalam (mai ritaya), Boko Haram ta kai harin ne a safiyar ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito cewa hukumar INEC na tsaka da tattarawa tare da sanar da sakamakon zaben cike gurbi na mazabar Yobe ta Gabas a majalisar dattijai lokacin da aka kai harin.
Sai dai Manjo Janar Abdulsalam ya bayyana cewa jami'an tsaro sun kai daukin gaggawa a cibiyar, inda suka fatattaki mayakan.
Gwamna Buni ya gamsu da zaben cike gurbi a jihar
Tun da fari, TV360 Nigeria ta ruwaito cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana gamsuwarsa kan yadda aka gudanar da zaben cike gurbi a mazabar Yobe ta Gabas a ranar Asabar.
Buni wanda ya kada kuri’a a rumfar zabe ta Bulturi-Yerimari da ke Buni-Gari a karamar hukumar Gujba, ya ce ya yi farin ciki da fitowar masu kada kuri’a.
Gwamnan ya kuma ce yankin da a da aka dai-daita su a halin yanzu suna zaune cikin zaman lafiya, kuma suna gudanar da harkokin yau da kullum yadda ya kamata.
Sojoji sun kama shugaban matasa a Ebonyi
A wani labarin kuma, sojoji sun kama wani shugaban matasa a karamar hukumar Afikpo da ke jihar Ebonyi a daren ranar da za a gudanar dazaben cike gurbi a jihar.
Jam'iyyar AFGA ta yi ikirarin cewa ana amfani da sojoji waje cin zarafin mutane a yayin gudanar da zaben a jihar.
Asali: Legit.ng