Da Ɗuminsa: Sojoji Sun Daƙile Harin 'Yan Bindiga a Makarantar Fasto Oyedepo a Kaduna

Da Ɗuminsa: Sojoji Sun Daƙile Harin 'Yan Bindiga a Makarantar Fasto Oyedepo a Kaduna

  • Sojojin Nigeria sun dakile wani hari da yan bindiga suka kai, Faith Academy, makarantar Bishop David Oyedepo da ke Kaduna
  • Mahaifiyar wani dalibi a makarantar ta tabbatar da afkuwar lamarin tana mai yiwa jami'an tsaro jinjina saboda kai dauki cikin gaggawa
  • Wani jami'in tsaro da ya tabbatar da lamarin ya ce yan bindiga sun kai hari makarantu biyu ne amma ba su yi nasara a Faith Academy ba

Sojojin Nigeria a safiyar ranar Litinin sun dakile harin da aka yi yunkurin kaiwa Faith Academy, wani makarantar sakandare mallakar cocin Living Faith Church Worldwide, da Bishop David Oyedepo ya kafa.

Daily Trust ta ruwaito cewa makarantar ba shi da nisa daga makarantar kwana inda aka sace dalibai da dama a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

Da Duminsa: Sojoji Sun Dakile Harin Da 'Yan Bindiga Suka Kai Marantar Bishop Oyedepo
Da Duminsa: Sojoji Sun Dakile Harin Da 'Yan Bindiga Suka Kai Marantar Bishop Oyedepo
Asali: Original

DUBA WANNAN: El-Rufai: Dalilan da yasa bai zai dace a kwatanta Nnamdi Kanu da Sheƙau ba

Yan bindigan sun kai hari ne a Bether Secondary School da Faith Academy a safiyar ranar Litinin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A yayin da sunyi nasarar sace dalibai a Bethel School, sojoji sun dakile harin na Faith Academy.

Wani jami'in tsaro ya tabbatar da cewa yan bindigan sun kutsa cikin harabar Faith Academy ta bayan katanga misalin karfe daya na dare amma sojoji tare da taimakon masu tsaron makarantar suka fatattake su.

Mahaifiyar dalibin makarantar ta jinjinawa sojoji

Wata mahaifiya da danta ke makarantar ta shaidawa majiyar Legit.ng cewa mahukunta makarantar sun umurci iyaye su tafi da yaransu gida sai dai yan ajin karshe da ke shirin rubuta jarrabawar fita.

Ta ce ana shirye-shiryen komawa da yan ajin karshen zuwa Barnawa a Kaduna ta Kudu inda ake tsammanin za su cigaba da karatunsu.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Sace Mata 13 a Hanyarsu Ta Zuwa Biki a Birnin Gwari

Ta yabawa jami'an tsaron bisa daukin da suka kai cikin gaggawa, tana mai cewa dukkan daliban da ke makarantar suna nan lafiya kuma an fitar da su daga harabar makarantar.

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige ya ce ba zai iya tabbatar da lamarin ba amma ya ce jami'an tsaro suna ta aikin dakile harin yan bindigan cikin dare.

Rundunar 'Yan Sanda Ta Tabbatar 'Yan Bindiga Sun Sace Mutane 8 a Zaria

A wani labarin, rundunar yan sandan Nigeria reshen jihar Kaduna, a ranar Lahadi ta tabbatar da sace mutane takwas daga rukunin gidajen ma'aikatan Cibiyar bincike kan cutar tarin TB da Kuturta da ke Zaria, jihar Kaduna, The Guardian ta ruwaito.

Vanguard ta ruwaito cewa mai magana da yawun rundunar, ASP Muhammed Jalige ya tabbatar da hakan cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi a Kaduna.

Jalige ya ce, a farkon daren Asabar misalin karfe 1.30 na dare, wasu da ake zargin yan bindiga ne masu dimbin yawa suka kai hari hedkwatar ofishin yan sanda da ke Saye a Zaria.

Asali: Legit.ng

Online view pixel