Kano: Yadda Wani Mutum Ya Aurawa Malaminsa Yaransa Mata 2 a Lokaci Guda, An Maka Shi Gaban Hisbah

Kano: Yadda Wani Mutum Ya Aurawa Malaminsa Yaransa Mata 2 a Lokaci Guda, An Maka Shi Gaban Hisbah

  • Hukumar Hisbah a jihar Kano ta sun tsitsiye wani mutum mai suna Umar Abubakar, wanda ake zargi da aurawa malaminsa yaransa mata biyu a lokaci guda
  • Mutumin dai ya dauki yaran zuwa kasarsa ta Nijar da nufin ganin 'yan uwansa amma sai ya bige da aurar da su ba bisa shari'a ba
  • An rahoto cewa ba su kadai ne 'yan uwan juna da ke auren Gausi Mustapha ba, harda wata uwa da 'ya'yanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rahotanni sun kawo cewa ana zargin wani uba mai suna, Umar Abubakar, da aurawa wani malaminsa, Gausu Mustapha, yaransa mata su biyu a lokaci guda a jihar Doso dake kasar Nijar.

Uwar rikon yaran ne ta yi karar Abubakar gaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, inda ta nemi a yi mata iyaka da mahaifin yaran wanda ke kokarin kwashe su don mayar da su hannun malamin.

Kara karanta wannan

An gano gawar 'yar jami'ar Najeriya a dakin kwananta

Matar wacce aka boye sunanta ta bayyana cewa ita matar kakan yaran ne, saboda rikonsu ya dawo hannunta bayan rasuwar mahaifiyarsu.

Wani mutum ya aurawa malaminsa yaransa mata 2
Yadda Wani Mutum Ya Aurawa Malaminsa Yaransa Mata 2 a Lokaci Guda Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda rikon yaran ya koma hannun mahaifinsu

A cewarta, kakansu wato mahaifin uwarsu da kansa ya damka mata yaran bayan ta kwanta dama, lokacin babbar tana shekaru biyu yayin da karamar ke da watanni 10 a duniya.

Sai dai kuma mahaifinsu ya karbe su a lokacin da suka yi shekaru 10 a hannunsu da nufin kai su wajen 'yan uwansa domin su san su a kasar Nijar, rahoton Aminiya.

Bayan shafe shekara guda ba tare da jin doriyar yaran ba, sai marikiyar suka yi karar mutumin a hukumar NAPTIP wanda rashin jin gamsasshen bayani kan inda yaran suke yasa suka rufe shi.

Amma bayan wani dan lokacin sun sake shi saboda yana da wasu manya a sama, kamar yadda marikiyar ta bayar da labari.

Kara karanta wannan

Yadda masu garkuwa da mutane suka kashe shugaban makarantar Kaduna, ya bar mata 3 da yara 13

Yadda muka samu labarin auren, uwar rikonsu

Matar ta ci gaba da bayyana cewa basu sake jin doriyar yaran ba sai bayan shekaru shida sakamakon sakon da babbar ta aika masu ta Whatsapp tana mai sanar da su inda suke.

Ta ce:

“To a hirar da muke ta yi da su ne suka shaida min cewa wai malamin ma ya aure su duk su biyun. Sannan sun yi rokona kan na taimaka na fitar da su daga hannun mutumin."
“Sai na nemi taimakon ’yan uwan mahaifin su da suke Nijar. Da na je sai suka sada ni da wani alkali a Doso inda ya sa aka gudanar bincika aka gano cewa Gausun yana wani gari wai shi Bulbul a kusa da Gishime."

Ta bayyana cewa a haka ne suka dukufa sai garin tare da jami'an tsaro saboda shi Gausun yana da mutanensa. An dai fito masu da yaran bayan an kai ruwa rana.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da matar aure ta kama mijinta yana bacci da mahaifiyarta a jihar Arewa

Bayan dawowarsu Kano na dan lokaci sai ga mahaifin yaran ya sake dawowa zai dauke su wanda hakan yasa marikiyarsu maka shi gaban hukumar Hisabah.

Hukumar Hisbah ta kama mahaifin yaran

Sai dai kuma, bayan da Hukumar Hisbah ta kama mahaifin yaran, ya sanar da cewar Gausu mutuminsa ne suna gudanar da ibadarsu a tare.

Ya ce ya fara aura masa diyarsa daya amma da suka rabu ne ya basa kanwar ta.

Yaran sun shaidawa jaridar Aminiya cewa ba su kadai bane 'yan uwan juna dake auren Gausu, hasalima akwai wata uwa da yaranta cikin matansa.

Wani mataki hukumar Hisbah ta dauka?

Shugaban hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Shaikh Aminu Daurawa ya tabbatar da lallai sun raba auren yaran da wannan malamin.

Ya kuma ce sun sa Abubakar ya rubuta wata takarda da hannunsa cewa ba zai sake daukar su ba balle ya mayar da su Nijar hannun mutumin.

Kara karanta wannan

'Yan makarantar Ekiti: An bar yaranmu da yunwa sannan ga duka, Iyaye

An daskarar da asusun Hisbah

A wani labarin kuma, mun ji cewa sakamakon wani kokari da ‘yan Hisbah suke yi na yaki da alfasha a jihar Kano, hukumar ta samu kan ta a matsala.

Aminu Ibrahim Daurawa ya fadawa TRT Hausa cewa wani Alkali ya bada umarni a rufe asusun hukumar Hisbah da ke banki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng